Shugaban kasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan ya mayar da martani ga mujallar The Economist, wadda ta wallafa labarin da ke cewa “A ceto dimokuradiyya” a Turkiyya, da kuma “Dole Erdogan ya sauka".
Shugaba Erdogan ya ce, “Ba za mu bari mujallun kasashen waje, wadanda manyan kasashe ke amfani da su a matsayin makami, su sauya siyasarmu ta cikin gida da kuma alkiblar mutanenmu ba”.
Mujallar the Economist ta Birtaniya ce ta wallafa wasu labarai da nufin suka ga shugaban Turkiyya, game da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisu da za a gudana ranar 14 ga watan Mayu.
Shugaba Erdogan yana takarar neman cigaba da shugabancin kasar, inda zai kara da ‘yan takarar jam’iyyun hamayya, Kemal Kilicdaroglu, da Muharrem Ince, da Sinan Ogan.
A zaben ‘yan majalisun kasar, jam’iyyu 24 ne, tare da ‘yan takara masu zaman kansu, su 151, suke neman kujerun majalisar dokokin Turkiyya mai mambobi 600.
Da yake tsokaci kan manufofin kasashen waje na Turkiyya, Shugaba Erdogan ya ce ta hanyar kokarin jami’an diflomasiyyar Turkiyya, kasar ta kaddamar da ayyukan jinkai da na kasuwanci mai cike da karfin ‘yancin ra’ayi.
Shugaban ya ce, “Ta hanyar kara yawa jami’anmu na kasashen waje daga 163 zuwa 260, mun zamo cikin kasashe biyar da suka fi yawan jami’an diflomasiyya a duniya”
A cewar Shugaba Erdogan, a yau Turkiyya tana tallafa wa kawayenta a duk lokacin da suke bukatarta, misali a kasar Libya da Syria. Mun ceto yankin Karabakh bayan shekaru 30 na mamayar kasar Armenia.
Haka nan, gwamnatin Turkiyya ta taka rawar gani wajen warware rikice-rikice a yankuna masu fama da fitintinu, kamar yarjejeniyar fitar da hatsi a yankin tekun Bahar Aswad.
Shugaba Erdogan ya ce, “A matsayinmu na kasa mai cike da tarihin nasarori, da sannu za mu cimma matakin da ya dace da mu cikin tsarin siyasa da gamayyar kasashen duniya.”
Sannan ya jaddace burinsa da cewa, “Muna fatan zuwan Karnin Turkiyya, lokacin da za mu daukaka nasarorinmu na diflomasiyya don kai wag a matakin fada a ji a duniya”.