A 1987 ne Turkiyya ta mika bukatar neman shiga Tarayyar Turai, kuma a 2005 ne aka fara tattauna batun. / Hoto: AA

Turkiyya na son habaka alakarta da Tarayyar Turai bisa doron "nagartattun manufofi", in ji Ministan Harkokin Wajen Turkiyya.

A yayin da yake gabatar a kasafin kudin ma'aikatar ga kwamitin kasafin kudi na majalisar dokoki, Hakan Fidan ya bayyana cewa Turkiyya ta kasance mai aiki tukuru don ganin ta shiga Tarayyar Turai, kuma tana ci gaba da dabbaka manufofi mau kyau don inanta hadin kai da tattaunawa a dukkan bangarori.

Fidan ya ce lokaci zuwa lokaci Tarayyar Turai na nesanta kanta daga nagartaccen shiri, na baya-bayan nan shi ne a rahotonta na shekara-shekara game da Turkiyya da ke son shiga kawancen.

Ya kara da cewa "Kalubalen da muke fuskanta na nuni da cewa dangantakar Turkiyya da Tarayyar Turai na da muhimmancin da bai kamata a mayar da ita ta biyan bukatar wasu mambobi ba.

"Babban abun da Turkiyya ke tsammani daga Tarayyar Turai shi ne "a dauki kwararan matakai" da za su sake farfadowa da inganta da Turkiyya da kuma burinta na zama mamban Tarayyar."

Da yake bayyana cewa "A bayyane yake karara matsayi da rawar da Turkiyya ke takawa wajen zaman lafiya da walwala", kuma hakan zai amfani Turkiyya da Tarayyar Turai, idan har Tarayyar ta dauki wannan abu da muhimmanci a dukkan al'amuranta da suka hada da bukatar Turkiyya na zama mamba.

Rahoton ya maimaita sukar da aka yi wa Turkiyya a shekarun da suka gabata kamar kan batun dimokuradiyya, hakkokin dan adam da bangaren shari'a, sukan da mahukuntan Turkiyya suka yi watsi da su.

A 1987 ne Turkiyya ta mika bukatar neman shiga Tarayyar Turai, kuma a 2005 ne aka fara tattauna batun.

A duk tsawon wannan lokaci, ana ta dakatar da tataunawar saboda hawa dokin naki da wasu mambobin Tarayyar Turai ke yi, saboda dalilai da ba su da alaa da cancantar Turkiyya na zama mamba, in ji Ankara.

Warware rikicin kasa biyu a Cyprus

Game da rikicin tsibirin Cyprus, Fidan ya ce babban tubalin adalci, tabbatacce kuma dorarren sulhu shi ne na a amince da 'yanci da wanzuwar Turkawan Cyrus a tsibirin, a girmama ikonsu, da ba su matsayon kasa da kasa iri daya da na kudancin Cyprus.

Ya kara da cewa "Idan akwai wani sulhu, zai zama tsakanin kasashe biyu ne, ba tsakanin al'ummu biyu ba, sannan matsayin bangarorin biyu zai zama iri daya mai matsayi daya, kafin a fara wani zama a teburi."

Fidan ya ce za su ci gaba da kare hakkokin Turkiyya da manufofi a tekunan Bahar Maliya da Bahar Rum, kuma suna son habaka danganta da Girka "Da manufa ta gaskiya bisa tubalin nagartaccen tsari".

Ya kuma ce "Alakarmu da Girka na karkata ga abubuwa masu kyau, tare a taimakon diplomasiyyar da aka dinga nunawa a baya-bayan nan."

Duk da kokarin diflomasiyya da tattaunawa, Arewacin Cyprus na Turkawa da Kudancin Cyprus na Girka sun dauki tsawon shekaru suna takaddama.

Turkiyya na goyon bayan warware rikicin ta hanyar aiki da manufofin kasashen biyu, sannan a girmama kowanne bangare d ayin adalci wajen daidaito a matakin kasa da kasa da tsibirin ke dashi.

Alakar diflomasiyya

Fidan ya ce suna kara karfafa dangantaka da kasashen Gulf ta hanyar ziyartar juna da shugabanni ke yi, kulla yarjeniyoyi da samar da dabarun karfafa hadin kan.

Ya kara da cewa cigaban alakar siyasa na da tasiri kan sauran batutuwa.

Fidan ya kuma ce "Adadin jarin kasuwanci tsakanin Turkiyya d akasashen Gulf shida ya ninka sama da sau goma sha biyu a shekaru ashirin da suka gabata.

A yayin ziyarar da shugaban kasarmu ya kai Saudiyya da Qatar da Hadaddiyar Daular Larabawa a watan Yuli an sanya hannu kan yarjeniyoyi, wadanda ke da muhimmanci kan wadannan matakai."

Ya kuma jaddada cewa suna bin tsari na kare martabar Yaman, kuma za a ci gaba da kokarin kawo karshen rikicin siyasa da na jin kai a kasar ta hanyar tattaunawa da shiga tsakani.

Game da dangantaka da Masar kuma, ya ce alakarsu ta shiga sabon shafi a 'yan watannin nan bayan sake nada jakadu a manyan biranensu.

Ya kara da cewa "Za mu fadada alakarmu ta hanyar tuntubar juna a ziyara a karkashin taskar fahimtar juna da manufa iri daya da gwamnatin Masar."

Da yake bayyana cewar an samu cigaba sosai a lakar Turkiyya da Aljeriya a shekaru uku da suka gabata.

Ya ce ana ci gaba da kokarin tabbatar da warware rikicin siyasar Libiya da zai kare hadin kai da mutuncin kasar, ya kuma bayar da dama ga tabbatar da zaman lafiya mai dorewa.

Fidan ya kuma jaddada cewar Turkiyya ta bayar da gudunmowa wajen zaman lafiya, cigaban tattalin arziki da zamantakewa a kasashen Afirka.

Ya kara da cewa Turkiyya da ta zama mamba 'yar kallo a Tarayyar Afirka a 2005, an bayyana ta a matsayin abokiya mai muhimmanci ga nahiyar a yayin babban taron AU a 2008.

Da yake bayyana yadda Ankara ke bayar da muhimmanci ga kulla alaka da Afirka, wanda aka bayyana a 2013, Fidan ya ce "Muna maraba da karbar Afirka ta zama mamban G20, mun goyi bayan hakan a wajen taron da aka yi a New Delhi a wannan shekarar."

TRT World