Dangane da batun shigar kasar Sweden NATO, Fidan ya ce majalisar dokokin Turkiyya ce za ta yanke hukunci a karshe. / Hoto: AA 

Kungiyar Tarayyar Turai EU ta dauki Turkiyya a matsayin ''kishiya a maimakon abokiyar hulda,'' sannan mambobin NATO ba sa la'akari da matsalolin tsaro da suka shafi Ankara, a cewar ministan harkokin wajen Turkiyya Hakan Fidan.

"Hakan ne ya sa Turkiyya ta samar da karin hanyoyin dogaro da kanta," in ji Fidan a yayin jawabinsa ga majalisar dokokin kasar a ranar Alhamis.

Ba zabi ba ne a gare mu, in ji Fidan, tare da jaddada cewa ya zama wajibi ga "rayuwar al'umma da kasar Turkiyya baki daya."

"Na yi imanin cewa, idan kungiyar ta dauki kwararan matakai da za su karfafa tsarin zama kasarmu mamba, hakan zai haifar da sabbin damarmaki ga bangarorin biyu," in ji shi.

Fidan ya jaddada cewa Turkiyya ta kuduri aniyar ciyar da tsarin hadewarta da kungiyar EU gaba, yana mai kari da cewe dole ne kungiyar ta nuna "muradin da ya dace kan hakan."

"Yana da matukar muhimmanci EU ta kawar da rashin hangen nesa da wasu mabobinta marasa kishi ke nunawa saboda son rai," in ji shi.

A cewar Ministan, abin takaici shi ne EU ba ta daukar matakan da za su karfafa wa Turkiyya gwiwa ba kamar yadda take yi wa sauran kasashe da ke neman zama mambobi a cikinsu,” in ji shi.

Kiran kwamitin hadin gwiwa don tattaunawa

A zaman taron kwamitin hadin gwiwar Turkiyya da EU karo na 80 da aka gudanar a ranar Alhamis, an bayyana bukatar yin karin tattaunawa a tsakanin gwamnatin Turkiyya da hukumomin EU, tare da ba da shawarar inganta yanayin ayyuka, ciki da har hada manyan tarukan diflomasiyya a Brussels.

A cikin wata sanarwar da suka fitar, shugabannin bangarorin biyu Ismail Emrah Karayel da Sergey Lagodinsky sun jaddada muhimmancin karfafa tattaunawa a ko wane bangare tsakanin Turkiyya da Tarayyar Turai.

An nuna ''gamsuwa'' kan taruka da kwamitin hadin gwiwa ke hadawa a-kai-a-kai inda aka hada tattaunawar da wasu wakilai ciki har da mataimakin ministan harkokin wajen Turkiyya Mehmet Kemal Bozay da Marko Makovec na hukumar kula da harkokin wajen Turai da Luis Romera Pintor na ofishin jakadancin Sifaniya da ke wakiltar fadar shugaban kasa da dai sauransu.

Wakilan biyu sun jaddada muhimmancin zurfafa hadin gwiwa wajen kasancewar Turkiyya mamba a kungiyar EU.

Kazalika sun bukaci a tabbatar da hanyoyin samar da mafita a hadin gwiwar ta fannonin da suka hada da bin doka da oda da dimokuradiyya da tattalin arziki da tsaro, da kuma nazari kan yakin Rasha da Ukraine da hanyoyin bunkasa makamashi da tsaron abinci.

Sun yi kira da a kafa kasashe biyu don samar da zaman lafiya mai dorewa tsakanin Falasdinu da Isra'ila, tare da neman a kawo karshen tashe-tashen hankula da ke faruwa da kuma kashe fararen-hula.

Turkiyya ta dade tana neman kujerar zama mamba a kungiyar EU, tun a shekarar 1987 ta bayyana muradinta, sannan a shekarar 2005 aka soma tattaunawa kan shigarta kungiyar.

A shekarun da suka gabata aka dakatar da tattaunawa saboda sanya batun siyasa da wasu mambobin EU suka yi, bisa wasu dalilai da suka danganta da alakar cancantar zaman kasar a matsayin mamba, a cewar Ankara.

Dangantakar NATO

Dangane da dangantakar da ke tsakaninta da kungiyar tsaro ta NATO, Ministan harkokin wajen Turkiyya Fidan ya bayyana cewa, kawance da huldar da ke tsakanin yankin Turai da tekun Atlantika sun kasance muhimman batutuwan da suka shafi manufofin harkokin wajen Turkiyya a kasa da shekaru 70 da suka gabata.

"Idan muka yi nazari kan manufofin da wasu kasashen NATO suka aiwatar a cikin 'yan shekarun nan, za a ga an samu sabani a goyon bayan da ake bai wa kungiyar PKK/YPG a Siriya da kuma takunkumin da aka kakaba wa Turkiyya a harkar tsaro," in ji shi.

Kan batun shiga kasar Sweden cikin NATO, Fidan ya ce majalisar dokokin Turkiyya za ta yanke hukuncin karshe.

Kasar Finland da Sweden sun nemi zama mamba a kungiyar NATO jim kadan bayan kaddamar da yaki da Rasha ta yi a Ukraine a watan Fabrairun shekarar 2022.

TRT World