Shugabar ƙasar Tanzania Samia Saluhu Hassan ta ce ƙasarta tana goyon bayan ƙoƙarin Turkiyya wajen warware taƙaddamomin ƙasa da ƙasa cikin lumana.
"Muna kuma goyon bayan tsagaita wuta nan-take don amfanin jama'ar Gaza. Haka kuma, muna goyon bayan a bayar da damar kai kayan agajin jinƙai," in ji Samia Hassan a yayin taron manema labarai a Fadar Shugban ƙasar Turkiyya bayan ta gana da Shugaba Erdogan a ranar Alhamis.
Ta ce Tanzania na sake jaddada ƙudurinta na inganta alaƙar amfanar juna tsakanin aƙsashen biyu.
Ta ce "Tabbas Turkiyya abokiya ce mai daraja, kuma ziyarata na tabbatar da yadda darajar ƙawancen take. Mun tattauna tare da gamsuwa sosai kan ci gaban da aka samu a ɓangarori daban-daban na dangantakarmu."
Haɓaka alaƙar diflomasiyya
Hassan ta ƙara da cewa ita da Erdogan sun tattauna kan haɓaka alaƙar diflomasiyya, musamman wajen samar da ci gaba a fannin zamantakewa.
Ta bayyana cewa yarjejeniyar za ta bayar da gudunmawa wajen haɓakar tattalin arzikin ƙasashen biyu.
"Na bayyana godiyata ga Turkiyya saboda alaƙar da ke tsakaninmu. Ina godiya gare su saboda taimako da gudunmawar da suke bai wa ɓangarorin kula da lafiya da ilimi a ƙasarmu. Ina miƙa godiya ta musamman gare su kan goyon bayan da suke ba mu na samar da kayan more rayuwa da ci gaban ɗan'adam," in ji ta.
Shugabannin biyu sun sanya hannu kan yarjeniyoyi guda shida, in ji shugabar ta Tanzania.
"Ana kai ƙwararrun Turkiyya zuwa Tanzania, ciki da manyan muhimman ayyuka."
Ta ce "Daga cikin waɗannan ayyuka akwai na layin-dogo, aikin jirgin ƙasa mai inganci, kuma na sake jaddada goyon bayan Tanzania na ganin an samu nasarar gudanar da waɗannan ayyuka. Idan aka tabbatar da su, za mu samu haɓaka a manufofinmu na ci gaba. Ministocinmu, ƙwararrunmu da dukkan ma'aikata za su haɗu su duba yadda za a haɓaka haɗin-kai a ɓangarorin da aka cim ma yarjejeniya."
Hadin kai a fannin kasuwanci da zuba jari
Hassan ta bayyana jin dadinta a wajen karbar bakuncin Tarin Hukumar Cigaban Tattalin Arzikin Tanzania-Turkiyya (JEC) kuma ta ce Tanzania na shirin tattaunawa da bangaren 'yan kasuwa masu zaman kansu da masu ruwa da tsaki a Turkiyya game da hadin kai a fannin kasuwanci da zuba jari."
Ta kuma yi tsokaci da cewa Tanzania za ta gudanar da taro a Istanbul a ranar Juma'ar nan da zai mayar da hankali kan sakonni uku.
Ta ce "Daya daga cikin sakonnin shi ne muhimmancin zuba jarin 'yan Turkiyya a Tanzania. Na biyu kuma, za mu duba da yin nazari kan irin kasuwancin da 'yan kasuwar Tanzania za su iya yi, matsayin da za su iya samu a kasuwanni da damarmakin da za su kawo ga kamfanonin Turkiyya da yadda za su ƙulla alaƙar kasuwanci da mu."
Hassan ta lura da cewar za kuma a tattauna kan harkokin sufuri, tattalin arzikin albarkatun teku, masana'antu, noma da yawon buɗe ido.
Ta kara da cewa Tanzania ta yi musayar ra'ayoyi da Erdogan kan manyan batutuwan yankuna da ma duniya baki ɗaya.
Hassan ta gode wa Erdogan sakamakon miƙa sakon ta'aziyyar mutuwar yara 'yan makaranta da ruwan sama ya yi ajali a Tanzania.
Ta bayyana cewa an cim ma kyakkayawan sakamako a ganawar da aka yi da Erdogan.
A yayin da take gayyatar Shugaba Erdogan zuwa Tanzania ta bayyana cewa "Na tabbata cewa tare da ƙoƙarinmu na hadin gwiwa, Tanzania da Turkiyya za su ci gaba da haɗa kai mai amfani da ƙarfi tare da cim ma bukatun juna."