Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya yi kira ga kasashen da ke ci gaba da bai wa Isra'ila makamai da su kawo karshen "laifukan da take aikatawa" a hare-haren da ta dauki tsawon watanni ana yi a Zirin Gaza na Falasdinu.
"Kasashen da ke ba da tallafin harsasai da makamai ga kisan kiyashin Isra'ila dole ne a yanzu su guji shiga cikin wadannan laifuka," in ji Erdogan yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa a Ankara babban birnin kasar a ranar Alhamis tare da takwaransa na Uzbekistan Shavkat Mirziyoyev.
Da yake tsokaci ga al'ummar duniya da ya ce ba su yi abin da ya dace ba don kawo karshen "kisan gilla" na Gaza, Erdogan ya kuma bukaci dukkanin ɓangarorin da suka san ya kamata da su yi abin da ya dace" don taimakawa wajen cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta cikin gaggawa a Gaza.
An lalata Gaza
Isra'ila dai na ci gaba da kai munanan hare-hare a Gaza tun bayan harin da kungiyar Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoba, duk kuwa da wani kudurin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya bukaci a tsagaita wuta cikin gaggawa.
An kashe Falasdinawa 36,600 tun daga lokacin a Gaza, yawancinsu mata da yara, yayin da wasu sama da 83,000 suka jikkata, a cewar hukumomin lafiya na yankin.
Watanni takwas da yakin Isra'ila, yankunan Gaza da dama sun zama kufai a cikin yanayin saka musu takunkuman hana shigar da kayan abinci da ruwa mai tsafta, da magunguna.
Kotun Ƙasa da Ƙasa tana tuhumar Isra'ila da aikata kisan kiyashi, hukuncin da ta yanke na baya-bayan nan ya umarci Tel Aviv da ta dakatar da ayyukanta a kudancin birnin Rafah, inda Falasdinawa sama da miliyan daya suke neman mafaka daga yakin kafin a mamaye shi a ranar 6 ga watan Mayu.