Shugaban Hukumar Leken Asiri ta Turkiyya da wasu manyan wakilan gwamnatin Iraki sun tattauna a babban birnin Bagdad kan hadin gwiwa wajen yaki da ta'addanci.
Shugaban Hukumar Leken Asiri ta Kasa (MIT) Ibrahim Kalin ya gana da shugaban kasar Iraki Abdul Latif da Firaministan kasar Mohammed Shia Al Sudani, in ji majiyoyin jami'an tsaro a ranar Talatar nan.
A yayin ganawar, bangarorin biyu sun tattauna kan batutuwa daban-daban kamar kokarin yaki da ta'addanci, barazanar 'yan 'ta'addar PKK, yiwuwar hada gwiwa wajen yaki da PKK, hadin kan tsaro, da ma ci gaba da aiki tare wajen yaki da kungiyar ta'adda ta Daesh, in ji majiyoyin.
A hare-haren ta'addanci da ta dauki shekara 35 tana kaiwa a Turkiyya, kungiyar PKK da Turkiyya da Amurka da Ingila da Tarayyar Turai suka bayyana a matsayin ta ta'addanci, ta yi ajalin sama da mutum 40,000 da suka haɗa da mata da yara ƙanana da jarirai.
Aikin Gina Hanyoyi Tsakanin Turkiyya da Iraki
Ganawar ta kuma tabo batun Aikin Gina Hanyoyi tsakanin Turkiyya da Iraki, a matsayin hadin kan tsaro da cigaban tattalin arziki.
Tare da hanyar mota da layin dogo masu tsayin kilomita 1,200 da ke tsakanin Turkiyya da Iraki, ana sa ran sbaon Aikin Cigaba na Hanya zai hade aikin Tashar Jiragen Ruwan Iraki ta Al Faw d ake yankin Gulf da Turkiyya.
An yi hasashen aikin zai lashe dala biliyan 17, inda ake sa ran kammala kashin farko na aikin a 2028. Ana sa ran kammala aikin a matakai uku - 2028, 2033 da 2050 - kuma a bude wa duniya kofofin Iraki ta hanyar amfani da Turkiyya.
Bangarorin biyu sun kuma tattauna kan halin da ake ciki a yankin Gaza na Falasdin da tasirinsa kan kasashe makota.
Isra'ila ta kaddamar da hare-hare kan Gaza da ke Falasdin bayan harin da Hamas ta kai wa Isra'ilan a ranar 7 ga Oktoba, inda ya zuwa yau ta kashe Falasdinawa 25,490 tare da jikkata wasu 63,354. An bayyana kashe kusan 'yan Isra'ila 1,200 sakamakon farmakan Hamas.
A yayin ziyarar tas aa Iraki, kalin ya kuma tattauna da wakilan kungiyoyin Shia da Sunna, da kuma wakilan jama'ar Turkmen.