Erdogan ya karbi shaidarsa ta zama shugaban kasa daga Kakakin Majalisar Turkiyya na wucin gadi Devlet Bahceli. / Hoto: AA

An rantsar da Recep Tayyip Erdogan a matsayin shugaban Turkiyya bayan an sake zabensa a zagaye na biyu na zaben kasar da aka gudanar a ranar 28 ga watan Mayu.

Bayan kammala rantsuwar a majalisar dokokin kasar a ranar Asabar, Erdogan ya kai ziyara Anitkabir, wurin da aka binne Mustafa Kemal Ataturk, wanda ya kirkiro Jamhuriyyar Turkiyya.

Nan gaba kadan, shugaban kasar zai gudanar da biki na musamman wanda manyan baki daga kasashe 78 za su halarta da kuma shugabannin kasashe 21 da firaiministoci 13 da ‘yan majalisa da ministoci.

Akwai wakilai daga kungiyoyin kasa da kasa da suka hada da NATO da Kungiyar Kasashen Turkawa OTS da Kungiyar Hadin kan Musulunci OIC da za su halarci bikin.

Da dare kuma Erdogan din ya shirya liyafar cin abinci a Fadar Cankaya, tsohon gidan da shugabannin Turkiyya ke zama.

Ana kuma sa ran zai sanar da majalisar ministocinsa bayan liyafar cin abincin, Erdogan ya samu nasara a zabe zagaye na biyu da aka gudanar a ranar Lahadin da ta gabata inda ya ci zaben da kashi 52.18.

Sa’annan abokin takararsa daga bangaren adawa Kemal Kilicdaroglu ya samu kaso 47.82, kamar yadda hukumar zaben kasar ta sanar da sakamakon zaben.

TRT World