Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya yi Allah-wadai da yunkurin kisan gillar da aka yi wa dan takarar shugaban kasar Amurka Donald Trump.
"Ina Allah wadai da yunkurin kisan gillar da aka yi wa shugaban Amurka na 45 kuma dan takarar shugaban kasa, Mr. Donald Trump," kamar yadda Erdogan ya rubuta a X a ranar Lahadi, bayan da wani dan bindiga ya harbi Trump ɗin a kunne a wani gangami yaƙin neman zaɓe a Amurka.
Erdogan ya miƙa saƙon jaje ga tsohon shugaban Amurka Trump, da iyalansa, da kuma magoya bayansa.
"Na yi imanin cewa, za a gudanar da bincike kan wannan harin ta hanya mafi inganci domin tabbatar da cewa an gurfanar da wadanda suka aikata wannan aika-aika gaban kuliya cikin gaggawa, don gudun kada a bar baya da kura kan zaben Amurka da zaman lafiyar duniya," kamar yadda shugaban na Turkiyya ya bayyana.
Erdogan ya ƙara da cewa Turkiyya na tare da ƙawarta Amurka a wannan lamari.
An fitar da tsohon shugaban mai shekaru 78 a duniya a ranar Asabar da jini a fuskarsa daga dandamali bayan harbin da aka yi a garin Butler na jihar Pennsylvania, yayin da aka kashe wanda ya yi harbin da wani mai kallo tare da jikkata wasu 'yan kallo biyu.
Dan takarar na jam'iyyar Republican ya daga hannu ga jama'a a yayin da aka riƙe shi domin tseratar da shi a guje, sannan ya ce bayan haka: "An harbe ni da harsashi wanda ya huda saman kunnena na dama."
Shugaba Joe Biden, wanda ke shirin fuskantar Trump a zaben da za a yi a watan Nuwamba mai cike da rudani, ya yi Allah wadai da wannan lamarin, ya kuma kara da cewa "irin wannan tashin hankalin ba shi da matusguni a Amurka."