Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya miƙa saƙon ta'aziyyarsa ga waɗanda girgizar ƙasa ta shafa a kudancin Turkiyya a ranar 6 ga Fabrairun 2023, shekara biyu kenan bayan faruwar bala'i mafi girma a ƙasar.
"Ina addu'a ga Allah Ya yi rahama ga 'yan uwa maza da mata 53,537 da muka rasa," kamar yadda Erdogan ya bayyana a shafinsa na X a ranar Alhamis, yayin da yake alhinin cika shekara biyu bayan wata girgizar ƙasa mai ƙarfi da ta kashe jumullar mutum 53,537 da kuma jikkata fiye da 107,000.
Yayin da yake tunawa da abin da ya faru, shugaban ya jaddada aniyar ƙasar ta sake gina garuruwan da lamarin ya faru da kuma taimaka musu.
"Tun daga ranar farko, mun haɗa kanmu a matsayin ƙasa da jama'a inda muka ce 'dukanmu ɗaya ne,' kuma ba mu taɓa janye goyon bayan da muke bayarwa ga yankunan da girgizar ƙasar ta shafa ba," in ji shi.
Shugaban Erdogan na Turkiyya ya jaddada cewa, za a ci gaba da kokarin sake gina garuruwan tare da jajircewa, aiki tukuru, da juriya har sai kowane dan kasa ya samu gidan da zai koma.
Erdogan ya kuma bayyana cewa za a ci gaba da tunawa da waɗanda suka rasu ta hanyar addu'o'i da kuma karatun Alkur'ani.
A ranar 6 ga wata Fabrairu, wata girgizar ƙasa mai ƙarfin maki 7.7 da 7.6 ta faɗa larduna 11 na Turkiyya waɗanda suka haɗa da Adana, Adiyaman, Diyarbakir, Elazig, Hatay, Gaziantep, Kahramanmaras, Kilis, Malatya, Osmaniye da kuma Sanliurfa.
Fiye da mutum miliyan 13.5 ne girgizar kasar ta shafa a Turkiyya, da kuma wasu da dama a arewacin Siriya.