A yayin da muke shiga ƙarni na biyu na zamowar Turkiyya Jamhuriyar, ƙasar ta zamo wata mai faɗa a ji a yankin," in ji Altun. Hoto: AA

Ana girmama Turkiyya a ƙasashen duniya kuma tana samun nasara a muhimmiyar rawar da take takawa, musamman a kan al'amuran da suka shafi yankin, ciki har da lamarin Gabas ta Tsakiya da kafatanin yankin Asiya, in ji daraktan sadarwa na ƙasar.

A wata maƙala da aka wallafa a Jaridar Daily Express ta Birtaniya da Interfax ta Rasha, Daraktan Sadarwar Fahrettin Altun ya ce taimakon jinƙai da matsayar siyasa da Shugaba Tayyip Erdogan ke jagoranta a kan lamarin Isra'ila da Falasdinu a baya-bayan nan sun tabbatar da ƙoƙrin Turkiyya da iyawarta a kan al'amuran duniya.

"Kamar yadda aka gani a kan sha'anin Ukraine da Karabakh da sauran al'amuran da suka shafi yankin, a yayin da muke shiga ƙarni na biyu na zamowar Turkiyya Jamhuriyar, ƙasar ta zamo wata mai faɗa a ji a yankin," in ji Altun.

Daraktan Sadarwar ya ce hukumomin ƙasa da ƙasa irin su Kwamitin Tsaro na MDD sun nuna cewa ba za su iya warware matsalolin duniya ba kuma ma sun rura wutar waɗannan matsaloli da ke ta’azzara rikice-rikice.

Altun ya bayyana buƙatar saamar da hukumomin ƙasa da ƙasa da suke da muradu irin na sabon ƙrnin da kuma duba kan ƙasashen duniya masu ƙara ƙarfi.

“Turkiyya tana amfani sosai da hanyoyin sadarwa a zamanance, kamar na jinƙai da diflomasiyya. A wajen warware matsalolin duniya da na yanki,” in ji shi.

“Rawar da Turkiyya ke takawa a Shirin Yarjejeniyar Hatsi ta nuna irin damarmakin da take da su a gaba na zama babbar hanyar samar da mafita wanda ya wuce mayar da hankali kan yanki gudaɗaya kacal, inda take shiga cikin al’amuran da suka shafi wasu yankunan musamman ma a Afirka.

Da yake jaddada aniyar Turkiyya na zama ɗaya daga cikin ƙasashe mafi muhimmanci masu faɗa a ji a duniya cikin sabon ƙarni, Altun ya ce ƙasar za ta samu ci gaba da gaggawa da kuma ƙwarin gwiwar cimma muradunta na shekarun 2053 da kuma 2071.

“An yi amfani da dukkan ƙirƙire-ƙirƙiren da aka samu ta dalilin fasahohin sadarwa da watsa labarai wajen tabbatar da ɗorewar wannan ƙuduri,” ya faɗa.

Ya ƙara da cewa “Jamhuriyar Turkiyya za ta ci gaba a kan turbarta ta bin dokoki da ƙa’idojin da ta shimfiɗa harsashinta a kai a dukkan fannonin da ake buƙata a zamanance.”

“Sabon ƙrnin Jamhuriyar zai zama Ƙarnin Turkiyya. Wannan ba wai ƙuduri ne ko wata manufa mai sarƙaƙiya da ba za a cimma ba; babban muradi ne da ya samo asali daga tarihi da hadin kan ƙasa da hikimar ƙasa da kuma nauyin zama ƙasar.”

Ya fayyace yadda zamantakewa da tattalin arziki da yankin da Turkiyya ta faɗa suka zamo manyan abubuwan da za su sa ta cimma waɗancan ƙudurori na sama.

“Sannan kuma, ƙaƙƙarfan shugabanci da diflomasiyya mai tsari da aniyar samar da al’umma mai kyau sun zama cikamakin ginshiƙan shiga ƙarnin Jamhuriya a matsayin Ƙarnin Turkiya.”

TRT World