Ƙoƙarin sauya zamani zuwa fasahar intanet ya sa 'ana ƙirƙirar sabon addini' - Shugaba Erdogan

Ƙoƙarin sauya zamani zuwa fasahar intanet ya sa 'ana ƙirƙirar sabon addini' - Shugaba Erdogan

Erdogan ya kuma buƙaci a ɗauki matakan kare aƙidun Musulunci daga rushewa sakamakon "yarda bin tsarin addini ta ƙirƙirarriyar fasaha."
Erdogan ya kuma buƙaci a ɗauki matakan kare aƙidun Musulunci daga rushewa sakamakon "yarda bin tsarin addini ta ƙirƙirarriyar fasaha." / Photo: AA

Fafutukar sauya zamani zuwa fasahar intanet na ƙoƙarin ƙirƙiro wani sabon addini da zai yi wa addinan Musulunci da Kiristanci da Yahudanci ɓarna, "musamman ma ga addinin Musulunci," kamar yadda Shugaban Ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi gargaɗi.

"Fafutukar mayar da duniya turbar intanet gaba ɗaya yana ƙoƙarin ƙirƙirar wani sabon addinin na ƙirƙirarriyar fasaha da zai iya lalata addinan na uku, musamman ma Musulunci," Erdogan ya faɗa a wani jawabi da ya gabatar a ranar Talata a taron Cibiyar Addini karo na 7 da aka yi a Ankara, babban birnin Turkiyya.

Erdogan ya kuma buƙaci a ɗauki matakan kare aƙidun Musulunci daga rushewa sakamakon "yarda bin tsarin addini ta ƙirƙirarriyar fasaha."

"Dole ne a ɗauki matakan gaggawa da kuma tabbatar da kare dukkan muradun Musulmai daga bin duk wani tsari na fasaha," ya ƙara da cewa.

TRT World