"A yayin da Amurka ke yaki sosai a madadin Isra'ila, kasashen yankin na iya neman hanyar hada karfi don mayar da martani." in ji Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan a ranar Larabar nan.
"Wadanda ba sa son su ga irin wannan abu a Gaza, a nan gaba, na iya yin gogayyar samun karfin iko da mallakar makamai." in ji Fidan, yayin zantawa da 'yan jarida a Ankara.
Ya ce "Gazawar kasashen duniya wajen yin katabus da nufin kawo karshen rikicin wadanda ba sa son su ga irin wannan abu a Gaza, a nan gaba, na iya yin gogayyar samun karfin iko da mallakar makamai.."
Da yake tunatar da cewa yakin ya yadu a wasu yankunan duniya daban, da suka hada da Tekun Maliya, ya kuma ce "A yankin, ba tare da duba ga batun Falasdin ba, kasashe daban-daban na da matsaloli da Amurka da kasashen Yamma."
"Wannan rikici na da bangarori daban-daban, a wasu lokutan yaki ne na leken asiri, yakin na soja, da ake samun fito na fito. Wannan rikici da ke ci gaba ya shafi dukkan bangarori.
Ya yi nuni da cewa Amurka na son kwace iko da Tekun Maliya, tana hada kai da Yammacin duniya don samar da kawancen sojojin ruwa sannan su fara kaddamar da farmakan hadin gwiwa.
A yayin bayanin nasa, Fidan ya kuma soki harin Isra'ila na baya-bayan nan kan Beirut, inda ta aikata kisan gilla ga babban jami'in Hamas, inda ya ce wannan abu rashin kyautawa ne.
"Idan wannan abu ya ci gaba da faruwa, to tabbas ba za a kawo karshen yakin ba. Sabanin haka kuma, idan ana son magance rikicin, sai an zauna an tattauna tare da biyan bukatun a kafa kasashe biyu."
Munafurcin Yammacin Duniya
Da yake bayyana cewa Amurka da wasu kasashen Yamma na bayar da cikakken goyon baya ga Isra'ila, wanda hakan babbar matsala ce ga kokarin warware rikicin, in ji Fidan, yana mai karawa da cewa amma kuma sabanin haka matsayinsu game da rikicin Rasha da Ukraine ya sha bam-bam, matsayin kasashen duniya game da Gaza tsagwaron munafurci ne.
Ya kara da cewa abubuwan da ke afkuwa a Gaza sun janyo faduwar mutuncin Yammacin duniya da kasashen Turai nan da nan.
Ya kuma bukaci cewa damuwa kan hana sake aikata kisan kare dangi a Gaza, na iya sanya kasashe su fara neman karfi da mallakar makamai a nan gaba.
Hadin kan yanki da kasashen Musulmi
Da yake tunatar da kokarin Turkiyya na kafa wata kungiyar tuntuba da za ta kunshi kasashen Musulmin yankin, Fidan ya ce "Hadin kanmu ya ba mu damar tabbatar da magana da murya daya."
"A yanayin da Amurka da kasashen Yamma suke goyon bayan isra'ila ba tare da wasu sharudda ba, amfani da karfin soji ba shi ne zabi mafi alfanu a yankin ba," in ji Fidan, yana mai nuni ga dabaru mabambanta da ya kamata a yi amfani da su wajen warware rikicin yankin.
Ya kuma bayyana cewa ya kamata a mayar da hankali kan Yammacin duniya don Kasashen Musulmi, yana mai fadin dole a dauki matakin ko za akalubalanci kasashen da ke goya wa Isra'ila baya.
Matsaya kan Hamas
Game da matsaya kan Hamas, ya tunatar da cewa babu wani sauyi tsakanin kafin 7 ga Oktona da bayan 7 ga Oktoba.
"Wadanda ba sa kallon Hamas a matsayin kungiyar ta'adda amma suke kallon gwagwarmayarta a matsayin tirjiya, jam'iyyar siyasa ko makamancin haka, na ci gaba da aiki da wannan ra'ayi nasu. Haka ma masu yi mata kallon kungiyar ta'adda, na ci gaba da rike wannan ra'ayi nasu."
A karkashin wannan batu, ya ce "Yana da muhimmanci da kar a kawar da idanu daga yadda ake kashe jama'ar Gaza ba tare da bambancewa ba."
Hadin kai da Iraki don yaki da 'yan ta'addar PKK
Game da yaki da ta'addanci da Turkiyya ke yi, ya ce Turkiyya da Gwamnatin Yanki ta Kurdawa (KRG) a arewacin Iraki na da damuwa game da 'yan ta'addar PKK.
"Muna da cikakken hadin kai da Erbil a bangaren yaki da ta'addanci, musamman batun PKK da ke damun mu gaba daya," in ji shi yana mai karin haske kan muhimmancin ci gaba da aiki da tsarin da aka assa a baya.
"Bukatar da muke da ita, ita ce a ci gaba da aiki da yarjejeniyar da aka kulla game da tsarin shugabanci tsakanin bangarorin biyu. Mun mayar da hankali wajen hana hadin kan PKK-PUK ya samu karfi a yankin," in ji shi.
Ya ce kira ga ci gaba da aiwatar da tsarin shugabancin da aka assasa na bayyana matsayin Turkiyya na aiki da karba-karbar shugabanci, ana hana 'yan ta'addar PKK da PUK su samu gindin zama a yankin.
Daduwar muhimmancin leken asiri
Hakan Fidan ya ce "Turkiyya na ci gaba da tsayawa kan wajabcin sake samar da wasu hanyoyin kai farmakai daga hukumar leken asirinta."
Da yake bayyana yadda aikin leken asiri yake da fadi, ya ce "martanin leken asiri, wanda ya hada da neman masu leken asiri da ke aiki don kalubalantar wani bangare, wani bangare ne na kwarewa. Dukkan wadannan bangarori na bukatar kokartawa."
Ya yi nuni da cewa an yi sauye-sauye da dama a Hukumar Leken Asirin Turkiyya, hakan na samar da kyakkyawan sakamakon a wasu kasashe, in ji shi. "Ana iya ganin nasarar Hukumar karara a Siriya da Iraki inda ake kai farmakai ba tare da sojoji ba, ta hanyar hadin gwiwa da kawaye da ke kasashen."