Yawan 'yan Turkiyya da ke ketare kuma suke taka rawa a zaben kasar suna kara yawa/ Photo:TRT World

Rashin samun karbuwa a ketare ya sa ‘yan Turkiyya da ke kasashen waje suna kara taka rawa a tsarin zaben kasarsu.

Jim kadan bayan gigizar kasa biyu da suka auku a Turkiyya da Siriya, kuma suka kashe mutum 55,000 tare da lalata dubban gidaje, ‘yan Turkiyya da ke ketare suka fara tara kayayyakin agaji suna tura su ga wadanda lamarin ya shafa.

Daya daga cikin kasashen da kayayyakin agaji suka fara shiga Turkiyya ita ce Jamus, inda sama da 'yan asalin Turkiyya miliyan uku ke zama.

Kuma a Jamus din ne firgicin kasancewa ‘yan Turkiyyan masu zama a ketare ya bayyana karara a lokacin da wasu suka cinna wuta kan kayayyakin da aka tara don kyautarwan, a jihar North Rhine-Westphalia da ke Yammacin Jamus.

A cikin wannan yanayin ne Turkiyya za ta gudanar da zaben shugaban kasa a watan Mayu, da kuma zabar jam’iyyar da za ta jagoranci kasar da ke yankin Mediterranean, mai yawan mutane miliyan 84, nan da shekara biyar.

Mene ne adadin kuri’un ‘yan Turkiyyan da ke ketare?

Kimanin ‘yan Turkiyya miliyan 6.5 ne suke zama a wasu kasashen. A cikinsu akwai mutum miliyan 3.28 da suka cancanci yin zabe a zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun da ke tafe.

Idan aka kwatanta su da masu zabe miliyan 60.9 da aka yi wa rijista a cikin Turkiyya, za a iya yi wa kuri’un ketare kallon ‘yan kadan.

Amman a zaben da kowa ke da damar nasara, kowace kuri’a na da muhimmanci, za ta iya tasiri mai karfi, kamar yadda aka gani a zaben shekarar 2018.

“Kuri’un ketare ba sa babban tasiri a sakamakon zaben, amma kuma suna karin haske sosai game da abin da ‘yan Turkiyya da ke kasashen waje ke tunani game da siyasar kasar da kuma makomar kasarsu,” in ji Sinem Cengiz, wani mai sharhi kan lamuran siyasar Turkiyya da ke zama a Qatar.

Za a gudanar da zaben mazauna ketare daga ranar 27 ga watan Afrilu zuwa 9 ga watan Mayu ne, a cewar hukumar koli ta zaben Turkiyya. A Turkiyya za a yi zaben ranar 14 ga watan Mayu.

Yawancin ‘yan Turkiyya da ke ketare suna zama ne a Yammacin Turai, inda ma’aikatan Turkiyya suka zauna a shekarun 1960 a cikin tsarin sake gini da ya biyo bayan yakin duniya na biyu.

Su ne bakin al’ummar Musulmai mafi girma a yammacin Turai.

A watan Agustan shekarar 2014 ne ‘yan Turkiyya da ke kasashen waje suka fara kada kuri’a a zaben shugaban kasar Turkiyya.

Dokar ta ba da damar zabe ga dukkan dan Turkiyya da ke wata kasa da suka haura shekara 18, kuma sunayensu ke cikin rijistar ofishin rijistar mutane ta kasar ko kuma ofishoshin jakadancin kasar.

Jamus ce a kan gaba a cikin kasashen da 'yan Turkiyya da ke ketare za su yi zabe, inda mutum miliyan 1.4 suka yi rijistar zabe a kasar.

Kasashen Faransa da Netherlands da kuma Beljiyom ne ke biye da Jamus din.

A kasar Jamus ne 'yan Turkiyya masu zabe daga ketare suka fi yawa/Photo:AP

Ta yaya salon zaben ketaren ke tafiya?

Yawan masu zabe na kasashen waje na dada karuwa a hankali yayin da hukumomi ke kara rumfunan zabe, inda ‘yan kasar da ke ketare za su iya kada kuri’a.

“Kafin shekarar 2014, ‘yan Turkiyya da ke son yin zabe dole su zo Turkiyya kafin su kada kuri’a.

"Amma ba da damar zabe daga waje ya kawo sauki a shekarar 2014 yayin da ‘yan Turkiyya da ke zama a kasashen waje suka samu damar kada kuri’a a ofisoshin jakadancin kasashen da suke,” in ji Cengiz.

Wannan karuwar yawan masu zabe a ketaren na faruwa ne a daidai lokacin da Ankara ke dada taka rawa a fagen diflomasiyya, kamar irin rawar da Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya taka wajen bude hanyar fitar da hatsin Yukrain kasashen waje a lokacin yakin Yukrain din da Rasha.

A shekarar 2014, an kada kuri’u rabin miliyan na masu zabe miliyan 2.8 da suka yi rijista daga wasu kasashen a zaben shugaban kasa.

Wannan ya faru ne saboda matsaloli na yadda aka shirya zaben don an kafa rumfunan zaben ne a birane, kuma yadda wadanda ba su taba zabe ba, ba su gane tsarin ba.

Duk da haka, Erdogan ya yi nasara da samun kashi 62.5 cikin 100 na masu zaben da ke ketare.

Yawan masu zaben ya karu a zaben ‘yan majalisa da aka yi a shekarar da ke biye da wannan shekarar inda aka kara yawan rumfunan zabe, kuma aka kara lokacin yin zaben. An kada sama da kuri’u miliyan daya.

Jam’iyyar Erdogan ta Justice and Development (AK) Party ce ta sake kasancewa a kan gaba.

A zaben raba gardama na shekarar 2017 wanda aka yi domin gyara yadda fadar shugaban kasa ke aiki, wadanda suka fito yin zaben sun kai miliyan 1.4.

A zabukan shugaban kasa da na ‘yan majalisa da aka yi a shekarar 2018, wadda Jam’iyyar AK ta sake ci da taimakon kawayenta, yawan masu zaben ketare da suka kada kuri’a ya kai sama da mutum miliyan uku.

Me yake sa mazauna ketare ke zabe?

Wata takardar da masu bincike Sebnem Koser Akcapar da kuma Damla Bayraktar Aksel suka rubuta ta ce ‘yan Turkiyya mazauna kasashen waje sun sake samun sabon muhimmanci ne a shekarun 2000, lokacin da Jam’iyyar AK ta gane muhimancinsu a wajen nuna karfin Ankara a fagen diflomasiyya.

A wannan lokacin ne Ankara ta kara kaimi wajen neman shiga kungiyar Tarayyar Turai.

Turkiyya ta kara yawan ofisoshin jakadancinta a kasashen duniya cikin shekaru 20 da suka wuce, inda ta kara yawan ofisoshin daga 163 a shekarar 2022 zuwa 236 a shekarar 2017.

Watakila rashin samun wakilci da ‘yan siyasa ‘yan asalin Turkiyya ke fuskanta a Turai shi ya sa ‘yan kasar mazauna kasashen waje suke kara taka rawa a zabukan Turkiyya.

Alal misali, a shekarun 1990, akwai ‘yan siyasa ‘yan Netherland ‘yan asalin kasar Suriname a kasar Netherlands sama da ‘yan siyasan Netherlands ‘yan asalin Turkiyya, duk da cewar ‘yan asalin Turkiyya sun fi yawa a karamar kasar ta Suriname.

Kasar Suriname da ke kudancin nahiyar Amurka tana da yawan mutane da ya kai sama da rabin miliyan.

Masu zaben ‘yan asalin Turkiyya da suka yi rijistar zabe a kasar Netherlands din sun kai sama da 260,000.

Kin jinin ‘yan asalin Turkiyya ya bayyana a lokacin da Birtaniya take neman ficewa daga kungiyar Tarayyar Turai a lokacin da ‘yan siyasa masu ra’ayin rikau suka yi ta karya cewar gungun baki ‘yan Turkiyya suna neman kai da Birtaniya.

“Bincike ya nuna cewar ‘yan Turkiyya da suke fuskantar wariya mai yawa a kasashen da suke za su fi tasirantuwa da tattaunawar kishin kasa da na kishin al’umma da ke fitowa daga kasashensu na asali.

Sai dai kuma ba duka ‘yan Turkiyyan da ke zama a Turai ke da wannan ra’ayin ba; ya kuma danganta ne ga yanayin zamantakewa da na siyasa na kowace kasar Turai,” in ji Cengiz.

TRT World