Afirka a Ankara: Tallafawa mata ta hanyar Gidan Afirka

Afirka a Ankara: Tallafawa mata ta hanyar Gidan Afirka

A matsayinsa na wata gada dake tsakanin Turkiye da Afirka, Gidan Afirka na da manufar zama wata kasuwar hajojin da matan Afirka suka samar da hannayensu.

Ankara, babban birnin Turkiye ya zama cibiyar siyasa da diplomasiyya. Amma a dukkan tsawon lokacin da wannan birni ya dauka na bunkasa, akwai wata kungiya da ta yi fice a birnin.

An kafa Gidan Al’adun Afirka da Kasuwar Sana’o’in Hannu, wanda aka fi sani da Gidan Afirka, don a dinga gudanar da bukukuwan murnar alakar Turkiye da Afirka, wanda ke da manufar da Mai Dakin Shugaban Kasar Turkiye Emine Erdogan ta kira “Gwaggwabar gudunmowa ga kwanciyar hankalin Afirka”.

Ziyarar da Emine Erdogan ta kai zuwa kasashen Afirka da dama tare da Shugaban Kasar Turkiye Recep Tayyip Erdogan ce ta sanya aka kafa Gidan Afirka.

Tuba Nur Sonmez, Mai Bayar da Shawara ga Shugaban Kasar Turkiye kuma jagorar wannan gida na raya al’adu na da ra’ayin cewa, tushen assasa wannan gida shi ne, bayan da Uwargida Emine Erdogan ta kusanci kasashen Afirka sosai, tare da fahimtar matsaloli, damarmaki da kuma bukatar kafa alkawari na gaskiya da shugabanni da al’umar Afirka.

Sonmez ta shaidawa TRT World cewa “Babbar manufar a nan ita ce, a taimakawa mata da yara kanana wadanda su ne matsin rayuwa ya fi shafa a Afirka, kamar rashin lafiya, yunwa, talauci, rashin ilimi, yake-yake… a taimaka musu su tsaya da kafafunsu,”. Ta kuma kara da suna gudanar da aikin karkashin aiyukan diplomasiya na mai dakin Shugaban Kasa.

Kasuwar baje-koli ga matan Afirka

Sonmez ta kuma ce “Muna sayen kayan da mata suka samar daga kasashen Afirka da dama mu kawo su mu hada su da masu saya a wajen baje-kolin da darajar da suke da ita,”

Babbar manufar shirin ita ce a mika wadannan kaya masu zubi mai kyau da nuna al’adun Afirka, ga masu saya a kasuwa.

Kamar yadda Sonmez ta zayyana, a lokacin da ake sayen wadannan kayayyaki daga wajen matan Afirka da arha a kuma sayar da su da tsada a wuraren sayar da kayayyaki a Turai, Gidan Afirka na da manufar kawo matan Afirka dake samar da kayayyakin zuwa kasuwar da kansu.

Sonmez ta kara da cewa “Kudaden da ake samu ana amfanida su wajen karfafa da gina matan Afirka,”

A karkashin sabon tsarin alakar Turkiye-Afirka dake karkashin manufar Ankara ta “yiwuwar samar da duniyar hada-hada”, hukumomi da kungiyoyi irin su Ma’aikatar Harkokin Waje, Kungiyar Masu Masana’antu da ‘Yan Kasuwa Mai Zaman Kanta (MUSIAD), Hukumar Hadin Kai da Aiyuka ta Turkiye (TIKA) da Kamfanin Jiragen Sama na Turkiye na bayar da gudunmowa, a yayin da malaman jami’o’i, kungiyoyin da ba gwamnati ba, ofisoshin jakadanci da kwararru ke gudanar da aiyuka don bunkasa matan Afirka.

Mashahuran maziyarta

A yayin da gidan ke wayar da kai da aiyukan da ake gudanarwa, shahararrun sunaye- musamman matan shugabannin kasashen Afirka- na ziyartar wannan gida a koyaushe tare da bayar da gudunmowarsu ga kokarin da ake yi.

Sonmez ta kuma ce “Jakadun kasashen Afirka, malaman jami’o’i a Afirka, ‘yan kasuwa da kungiyoyin da ba na gwamnati ba wani bangare ne na Gidan Afirka.”

Daga cikin wadanan mutane akwai Ndileka Mandela, jikar Nelson Mandela wadda ta gabatar da makala mai taken “Aiyukan Mandela a 2019’; Ana Dias Lourenco, matar Shugaban Kasar Angola; da Aissata Issoufou, matar Shugaban Kasar Nijar.

A lokacin da take ziyartar gidan, Mandela ta bayana cewa Afirka ta Kudu na da abubuwa da dama da za ta koya daga wajen Turkiye,inda uwargidan Shugaban Kasar Angola kuma ta ce ta yi matukar farin ciki da yadda aka samar da wannan waje dauke da kayan da aka samar da hannu a Afirka.

Sonmez ta tunatar da cewa “Ta bayyana cewa ta ji kamar tana gida ne kan yadda ta ga dukkan kayan. Ta yi murna sosai saboda tsintar kanta a tsakiyar hasken Afirka.”

Haka zalika, wannan gida na da manufar samar da hanyoyin da za a shigar da daliban Afirka cikin al’umun Turkiye da rayuwar zamantakewar Turkiye, ta hanyar tallafa musu su zama suna cudanya da al’umunsu, karfafa musu gwiwa da su zauna a gida tare da samar da kayayyakinsu.

“Muna da wuraren da za su iya gudanar da taro, yin karatu da kuma dakin karatu dake dauke da litattafan da suka shafi Afirka.”

A yayin da Gidan Afirka ke da manufar bunkasa alakar Turkiye-Afirka a bangarori da dama, gidan na kuka kokarin sanyaya zukatan matan Afirka, a matsayin nuna kawance.

Sonmez ta ci gaba da cewa “Tabbas, a cikin kankanin lokaci ba za mu iya zayyana dukkan aiyukan da muke yi don Afirka ba”, ta kuma kara da cewa za a ci gaba da dukkan wannan kokari.

Sonmez ta rawaito uwargidan Shugaban Kasar Turkiye Emine Erdogan na cewa “Dadadden kawancenmu da Afirka ba ya tsaya a kan takardun litattafan tarihi ba ne kawai, godiya ga kokarin da bangarorin biyu ke yi. Mun sauya kawnacenmu da ya samo asali a tarihi zuwa tekun kawance da biyayya ga juna,”

TRT World