Turkiyya ta shiga kungiyar kawaye da wakilai na musamman na Babban Taron Kasa da Kasa Kan Yankin Manyan Tafkuna (ICGLR) daga watan Mayu, a cewar Ma’aikatar Harkokin Wajen Kasar.
A sanarwar da ma’aikatar ta fitar a ranar Laraba ta bayyana cewa “Manufarmu ta kawance da Afirka na da babban matsayi a kundin manufofofin harkokin waje kan ci-gaba da gina dan adam na Turkiyya. A wannan gaba, inganta alakarmu da kungiyoyin shiyyoyi a nahiyar Afirka na daga abubuwan da muka bai wa fifiko.”
Sanarwar ta kara da cewa ICGLR na taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya, ci-gaba da tsaro.
Ma’aikatar ta ce “Karbar mu a wannan kungiya za ta kawo sabon salo ga manufarmu ta hadin kai da Afirka, hadin kanmu da Yankin Manyan Tafkuna, sannan a kulla dangantaka ta kusa da ICGLR, gami da tallafawa ayyukan kungiyar.”
Manufar ICGLR ita ce tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasashen Angola, Burundi, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, Jamhuriyar Kongo, Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo, Kenya, Uganda, Ruwanda, Sudan ta Kudu, Sudan, Tanzaniya da Zambiya.