Bayan shiga zaben 2018 karkashin babbar jam’iyyar adawa, dan siyasar Turkiyya Muharrem Ince a wannan karon ma zai sake yin takara a karkashin sabuwar jam’iyyarsa mai suna ‘Memleket Party’.
Kafin Muharrem Ince ya kafa tasa jam’iyyar, dan siyasar na da dogon tarihin wakiltar jam’iyyarsa ta CHP musamman ma yadda ya zama dan takararta a zaben shugaban kasa na 2018.
A fafatawar da aka yi, Ince ya samu sama da kaso 30 na kuri’un da aka jefa a zaben na 2018, inda ya zama na biyu bayan dan takarar AKP Recep Tayyip Erdogan wanda ya samu kaso 53 cikin dari.
Shuhurarsa a jam’iyyar CHP da kuma durkushewarsa duk sun faru ne a garin Elmalik na lardin Yalova da aka haife shi a ranar 4 ga Mayun 1964.
A Yalova, Ince ya rike mukamai daban-daban a kungiyoyin da ba na gwamnati ba, inda yana da shekara 38 a 1990 ya yanke shawarar tsunduma siyasa wanda ya zama mamban majalisar dokoki mai wakiltar Yalova kuma har zangon mulki hudu.
A matakin yankinsa, Ince ya taba zama shugaban Kungiyar Masu Ra’ayin Tunanin Ataturk, ya kuma taba zama shugaban yada labaran kungiyar kwallon kafa ta Yalovaspor.
Takarar Shugaban Kasa, Baraka a jam’iyyar CHP
Kafin mutumin mai shekara 58 ya shiga harkokin siyasa, aikin da yake sha’awa shi ne koyarwa.
Ya kammala digirin farko a Jami’ar Uludag (Jami’ar Balikesir a yanzu) a sashen nazarin koyo, koyarwa da tarbiyya. Ya yi aikin koyarwa da ma zama shugaban makaranta a makarantu daban-daban.
Ince ya yi takarar zama shugaban CHP inda aka zabe shi mataimakin shugaban jam’iyyar Kemal Kilicdaroglu, mukamin da ya rike a tsakanin 2010 da 2014.
A shekarun 2011 da 2013 an sake zabar Ince a wannan mukami. Ya yi murabus a watan Agustan 2014 inda aka maye gurbin sa da Levent Gok. Ince na da mata mai suna Ulku da dansu daya, Arda.
A zabukan gama-gari na 2014 Ince ya taka rawa wajen goyon bayan magajin garin Yalova Vefa Selman.
Rikici tsakanin Ince da CHP ya kara karfi ne bayan da jam’iyyarsa ta fadi a zaben shugaban kasa a 2014.
Ince ya fara suka da kakkausar murya ga shugaban jam’iyyar na yanzu Kemal Kilicdaroglu da kuma dan takarar hadin gwiwa na CHP da MHP Ekmeleddin Ihsanoglu da Erdogan ya kayar a zaben.
Nan da nan sai Ince ya bayyana yana son zama shugaban jam’iyyar CHP.
A wani taron manema labarai da ya kira a 2014, Ince ya ce ba zai bar jam’iyyar CHP ta kunyata a idanun jama’ar Turkiyya ba, kuma wasu ‘yan tsiraru masu kama-karya ne ke shugabancin jam’iyyar.
Ya yi takarar shugabancin jam’iyyar amma ya sha kaye a babban taronta na 2014 inda ya samu kuri’u 415, abokin takararsa Kilicdaroglu kuma ya samu kuri’u 740.
Amma duk da haka jam’iyyar CHP ta tsayar da Ince takara a zaben shugaban kasa na 2014, kuma Kilicdarolgu ya goyi bayan takarar tasa.
Ince ya fara gangamin zaben 2018 da wani taron siyasa a Yalova da taken “Amintar da Turkiyya, Sai Muharrem Ince”.
Amma a karshe Erdogan ya kayar da shi a zaben da aka gudanar. Erdogan mai ci a yanzu ya samu kaso 52.6 yayin da Ince ya samu kaso 30.64 na kuri’un da aka jefa.
Bayan babban taron CHP karo na 37, Ince ya sanar da zai kafa sabuwar jam’iyya mai suna Memleket Party a watan Satumban 2020.
A watan Janairun 2021 ya sanar da murabus dinsa daga CHP a hukumance.