Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya shirya ziyartar Ethiopia a ranar 3 ga Agusta, 2024, domin tattaunawa da Firaministan kasar Abiy Ahmed da Ministan Harkokin Waje Taye Atske Selassie, in ji wata sanarwa da Maikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta fitar.
A yayin ziyarar ta Ethiopia, Ministan Harkokin Waje Fidan zai tattauna kan alaƙar kasarsa da Ethiopia da kuma kokarin sulhunta kasar da Somalia da ma sauran batutuwan yankin.
A watan da ya gabata, Hakan Fidan ya karbi bakuncin takwarorinsa na Ethiopia da Somalia a Ankara inda dukkan su ukun suka sanya hannu kan wata sanarwa ta bayan taro d ake bayyana an yi 'ganawa da aminci, kawance da inganta alaka a nan gaba'.
A yayin ganawar ta watan Yuli, Ministocin Ethiopia da Somalia sun tattauna kan hanyoyin bangance bambance-bambancen da ke tsakanin su "ta hanya mai kyau ga kowanne bangare" kuma sun amince su sake gana wa a ranar 2 ga watan Satumba a Ankara.
Ƙawancen diflomasiyya da Turkiyya
Alakar diplomasiyya tsakanin Turkiyya da Ethiopia, wadda na da muhimmanci a Manufofin Turkiyya na Hadin Kai da Afirka, ta samo asali tun kafin Turkiyya ta zama Jumhuriya, musamman ma shekarar 19896.
An samar da Ofishin Jakadancin Turkiyya a Addis Ababa 1926, inda a 1933 aka bude Ofishin Jakadancin Ethiopia a Ankara. Duk da cewar a 1984 an rufe Ofishin Jakadancin Ethiopia da ke Ankara saboda sauyin gwamnati, an sake bude shi a 2006,
Alaka tsakanin Turkiyya da Ethiopia ta zurfafa ta hanyar tuntuba da ziyartar juna, wadanda ke kasancewa cikin yanayin abota mai kyau.
Ƙarfin kasuwanci
Yawan jarin kasuwanni tsakanin kasashen biyu wanda a shekarar 2000 yake dala biliyan 27, a 2023 ya kai dala biliyan 345.
Ana da burin kara wannan wa'adi zuwa dala biliyan ɗaya nan da shekaru biyar. Turkiyya na daga cikin kasashe hudu na kan gaba da suke zuba jari kai tsaye a Ethiopia, inda kamfanonin Turkiyya na haɓaka a kasar.
Rikicin Ethiopia da Somalia
Ethiopia, kasa mafi yawan jama'a a duniya da ba ta da iyaka da teku, ta rasa hanyarta ta zuwa teku bayan da Eritrea ta samu 'yancin kanta a 1991.
Samun iyakar Tekun Bahar Maliya ya zama batun tattalin arziki mai muhimmanci ga Ethiopia.
A ranar 1 ga Janairun 2024, Firaministan Ethiopia Abiy Ahmed da Shugaban Kasar Somaliland sun sanya hannu kan yarjejeniyar Fahimtar Juna.
A yayin sanya hannun, Shugaban Kasar Somaliland ya bayyana cewa Ethiopia za ta zama kasa ta farko da ta amince da Somaliland a matsayin 'yantacciyar kasa, sanarwar da ta janyo mayar da martani daga Somalia da ma kasashen duniya.
Gudunmawar Turkiyya don warware rikicin
A ranar 8 ga Mayu, Jadan Musamman na Firaministan Ethiopia Abiy Ahmed, Mulatu tTeshome Wirtu tare da Ministan Harkokin Wajen Ethiopia sun samu tarba daga Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan.
A yayin ganawar, Ethiopia ta nemi goyon bayan Turkiyya game da rikicin da take yi da Somalia.
A matsayin mai shiga tsakani da aka amince da ita, Turkiyya a karkashin shugaba Erdogan ta fara ayyukan shiga tsakani. Ministan Harkokin Waje Fidan ya gana da takwarorinsa na Ethiopia da Somalia, a lokacin da ya karbi bakuncinsu a ranar 1 ga Yuli a Ankara.
Wannan ne karo na farko a cikin watanni da dama da ministocin harkokin wajen kasashen biyu suka bayyana a hotuna tare, suka kuma fitar da sanarwar hadin gwiwa inda suka yi fatan za su warware rikicin nasu ta hanyar lumana. Sun kuma ce za su gana a Ankara a ranar 2 ga Satumba.
Kasashen duniya sun yaba kokarin Turkiyya na tabbatar da sulhu mai dorewa tsakanin kasashe a loakcinda ake rikice-rikice a yankin.