Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan da Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken sun gana a Ankara domin tattaunawa kan halin da ake ciki a Gaza.
Fidan da Blinken sun tattauna kan matsalolin da suka shafi yankuna da kuma kasashen biyu.
Sakataren Harkokin Wajen na Amurka ya kai ziyarar ba-zata a ranar Lahadi zuwa Gabar Yamma da Kogin Jordan, inda ya tattauna da Shugaba Mahmoud Abbas.
Ziyarar ba-zatar da ya kai ba ta tsaya a nan ba inda ya kuma je Iraki da Cyprus.
Sai dai a daya bangaren, mambobin kungiyar matasa ta Turkiyya sun taru a kusa da ofishin harkokin wajen Turkiyya domin yin zanga-zanga kan zuwan na Blinken.
Mutanen sun rike tutocin Turkiyya inda gomman masu zanga-zangar suke ta ambatar: “Blinken, mai kashe mutane, ka fita daga Turkiyya.”
Sai dai dakarun Turkiyya sun shiga lamarin domin gudun ya kara fadada.
Bala’in rashin jinkai a Gaza
Rundunar sojin Isra’ila ta kaddamar da hare-hare ta sama da kasa a Gaza bayan harin ba-zata da Hamas ta kaddamar a ranar 7 ga watan Oktoba.
Akalla Falasdinawa 9,770 Isra’ila ta kashe, daga ciki har da yara 4,800 da mata 2,550.
Isra’ila kuma zuwa yanzu mutum 1,600 aka kashe kamar yadda hukumomi suka tabbatar.
Baya ga adadin wadanda suka rasa ransu da rasa muhalkansu, kayayyakin abinci sun kusan karewa ga jama’a miliyan 2.3 da ke a Gaza sakamakon kawanyar Isra’ila.