A wani kalubale kai tsaye ga kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, Erdogan ya nuna shakku kan rashin daukar matakin da suka dace wajen fuskantar kisan kare dangi a Gaza. Hoto: AP

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya matsa wa shugabannin kasashen duniya lamba da su amince da Falasdinu a matsayin kasa mai cin gashin kanta.

"Ina gayyatar kasashen da har yanzu ba su amince da Falasdinu ba da su tsaya kan dama ta tarihi a wannan mawuyacin lokaci da kuma amincewa da kasar Falasdinu cikin gaggawa," in ji Shugaba Erdogan a cikin jawabinsa ga Majalisar Dinkin Duniya a New York ranar Talata.

Erdoğan ya kara da cewa, dole ne a daina jinkirin samar da kasar Falasdinu mai cikakken 'yanci, tare da Gabashin Kudus a matsayin babban birninta da kuma tabbatar da yankinta.

Shugaban na Turkiyya ya kuma bayyana rashin jin dadinsa kan yadda Majalisar Dinkin Duniya ta kasa daukar kwararan matakai na kawo karshen tashe-tashen hankula, yana mai jaddada cewa kungiyar ta kara yin kasa a gwiwa.

"A cikin 'yan shekarun nan, Majalisar Dinkin Duniya ta kasa aiwatar da aikinta na tushe, sannu a hankali tana rikidewa zuwa tsarin da ba shi da inganci, mai wahala, da rashin aiki," in ji Erdogan, yana mai jaddada bukatar yin kwaskwarima a cikin duniya.

Da ya karkata akalarsa kan halin da ake ciki a Gaza, Shugaba Erdogan ya yi Allah wadai da matakan da Isra'ila take dauka.

"Sakamakon hare-haren da Isra'ila ke kaiwa, Gaza ta zama makabartar yara da mata mafi girma a duniya," in ji shi, yana mai jaddada munanan asarar rayukan fararen hula da ake samu.

Erdogan ya kuma yi kakkausar suka ga kafafen yada labarai na kasa da kasa, inda ya zarge su da rufe ido kan kisan da sojojin Isra'ila ke yi wa 'yan jarida.

"Ga kungiyoyin watsa labarai na kasa da kasa, ina tambaya: Shin ba a kashe 'yan jaridun a shirin talabijin da ake watsawa kai tsaye ba, kuma abokan aikinku Isra'ila ne suka kai farmaki ofishinsu?"

"Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta yi watsi da muhimman hakkokin bil'adama, tana aiwatar da kisan kiyashi a fili ga wata al'umma tare da mamaye yankunansu mataki-mataki. Falasdinawa suna amfani da halattaccen 'yancinsu na tsayin daka kan wannan mamaya."

"Me kuke jira don kawo karshen kisan kiyashin da ake yi a Gaza?"

A wani kalubale kai tsaye ga kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, Erdogan ya nuna shakku kan rashin daukar matakin da suka dace wajen fuskantar kisan kare dangi a Gaza.

"Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, me kuke jira don dakatar da kisan kiyashin da ake yi a Gaza, ku ce 'ya isa' ga wannan zalunci, wannan dabbanci?"

Erdogan ya kara da cewa, ba kananan yara kadai ba, har ma da tsarin Majalisar Dinkin Duniya na mutuwa a Gaza.. Gaskiyar dabi'un da Kasashen Yammacin Duniya ke ikirarin karewa suna mutuwa.

Ya kuma yi kakkausar suka ga wadanda ke da alhakin haddasa rashin zaman lafiya a yankin.

"Me kuke jira don dakatar da wannan hanyar tsari na kisan kiyashi da ke jawo duk yankin cikin yaƙi don burin siyasa?" Erdogan ya tambaya.

"Kamar yadda kawancen bil'adama ya dakatar da Hitler shekaru 70 da suka gabata, dole ne a dakatar da Netanyahu da masu goya masa baya ta hanyar haɗin gwiwar bil'adama."

TRT World