"Ba za mu sayi wani abu ba kuma za mu jefar da wanda muka saya," in ji shugaban majalisar dokokin Turkiyya Numan Kurtulmus. / Hoto: AA

Majalisar dokokin Turkiyya za ta daina amfani da kayayyakin da kamfanonin da ke goyon bayan hare-haren da Isra'ila ke yi, suka samar," in ji shugaban majalisar.

A yayin da yake jawabi a wajen wani taro a yankin Ordu na arewacin Turkiyya, Numan Kurtulmus ya bayyana cewa "A Babbar Majalisar Dokokin Turkiyya, ba za a sake amfani da duk wasu kaya da aka samar a kamfanonin da ke goyon bayan hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza ba."

Kurtulmus ya ƙara da cewa "Daga yanzu ba za mu sake sayen wani abu daga gare su ba, kuma za mu jefar da wanda muka riga muka saya."

Isra'ila ta kaddamar da hare-hare ta sama da ta ƙasa kan Zirin Gaza bayan da ƙungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta kai mata wani hari a kan iyaka.

Sakamakon rikicin, aƙalla Falasdinawa 10,328 da suka hada da yara ƙanana 4,237 da mata 2,719 aka kashe. 'Yan Isra'ila da aka kashe kuma sun kai 1,600.

TRT World