Kudirin ya nuna cewa Turkiyya za ta jagoranci gamayyar dakarun Combined Task Force-151 a karo na bakwai daga watan Yuli. / Hoto: Reuters

Majalisar Dokokin Turkiyya ta amince da wani kudirin doka wanda zai bayar da damar tura sojojin ƙasar zuwa Somaliya na tsawon shekara biyu domin tallafa wa ƙasar yaƙi da ta’addanci da sauran barazana duk a ƙarƙashin yarjejeniyar da Turkiyya ta yi da Somaliya kan tsaro.

Kudirin wanda Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya saka wa hannu, ya bayyana cewa Turkiyya ta jima tana bayar da horo da taimako da kuma shawarwari ga Somaliya sama da shekara goma domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma taimakawa wurin yin garambawul ga tsarin tsaron ƙasar da yaƙi da ta’addanci.

Kudirin ya bayyana cewa tun daga 2009, sojojin Turkiyya ke ta ƙoƙari domin yaƙi da ‘yan fashin teku da fashi da makami a Tekun Aden, da ke gabar tekun Somalia (ban da yankin ruwan Somalia), da tekun Larabawa da kuma yankunan da ke makwabtaka da su.

Tallafin ya ta'allaka ne kan Yarjejeniyar Murkushe Ayyukan Ta'addanci da ke adawa da amincin zirga-zirgar jiragen ruwa da kuma kudurin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya na Dec.16, 2008.

A baya-bayan nan ne majalisar dokokin Turkiyya ta kara wa'adin a ranar 17 ga watan Janairu na tsawon shekara guda.

Yanayin Tsaron Somaliya

Kudirin ya nuna cewa Turkiyya za ta jagoranci gamayyar dakarun Combined Task Force-151 a karo na bakwai daga watan Yuli.

Ta jaddada cewa duk da samun isassun ma'aikata da kayan aiki, jami'an tsaronSomaliya ba su kai matsayin da ake bukata ba saboda kalubalen tattalin arziki.

Gwamnatin Somaliya na son kula da yankunan teku da kuma hada albarkatun kasa cikin tattalin arziki domin inganta karfin jami'an tsaronta da sauran cibiyoyin gwamnati.

AA