Daraktan Sadarwa na Turkiyya Fahrettin Altun Fahrettin Altun ya caccaki mujallar The Economist, wadda ake wallafawa a Birtaniya, inda take nuna kyama ga Turkiyya da shugaban kasar Recep Tayyip Erdogan.
"Muna bayyana taiakcinmu kan yadda kafafen watsa labaran Yammacin Duniya suke nuna kyama ga Turkiyya da Shugaba Erdogan gabanin zaben 14 ga watan Mayu. Muna kallon yadda suke labarai game da kasarmu cike da mamaki," in ji Altun a sanarwar da ya fitar ranar Alhamis.
"A yayin da kasarmu ta fita daga kangin bauta, muna sanya ido kan yadda hare-haren da kafofin watsa labaran Yamma suke karuwa. A lokacin da Shugaba Recep Tayyip Erdogan yake bayar da muhimmanci game da cigaban kasarmu da kuma kin bari su tursasa mana, sun yi watsi da tsarin bayar da labarai cikin adalci sun zama 'an watsa jita-jita."
Ana kallon mujallar The Economist a matsayin wata kafa da ke goyon bayan kasashen Yamma wajen watsa labaran da ba su dace ba game da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki da za a yi a Turkiyya.
A babban labarin da ta wallafa ranar Alhamis, ta ced: "Dole Erdogan ya sauka daga mulki!"
Altun ya ce Turkiyya "ba sa'ar" kasashensu ba ce kuma "ta san abin da ya kamata ta yi".
"Kasarmu ta shirya bayar da mamaki, kuma ana yin wasu abubuwa ne da nufin dakushe zaben 14 ga watan Mayu, wanda za mu yi cikin tsari da manufofinmu," a cewarsa.