Kwamitin Harkokin Waje na Majalisar Dokokin Türkiye ya amince da kudirin dokar neman sahhalewa kasar Finland ta zama mamba a kawancen NATO.
Mataimakin Ministan Harkoki Wajen Türkiye Burak Akcapar ya yi jawabi ga ‘yan majalisar game da wannan kudiri.
Ya ce “Muna da imanin zama Finland mamba zai karfafi kawancen NATO, zai bayar da gudunmowar daukar nauyin magance barazana, zai taimaka wajen kara karfin NATO, da karfafa tsaron yankuna da kuma kokarinmu na yaki da ta’addanci.
Muna kuma kallon cewa kawancenmu da Finland zai bayar da gudunmowa wajen cigaban dangantakar da ke tsakaninmu.”
Akcap ya tunatar da cewa Finland ta mika bukatar neman shiga kawancen NATO a watan Mayun bara, inda ya kuma yi kira ga Swidin da Finland da su duba damuwar Türkiye kan sha’anin tsaro, sannan su fara daukar matakai albarkacin hadin kan da ke tsakaninsu.
Mataimakin ministan ya kuma ci gaba da cewa Swidin da Finland sun dauki kwararan matakai da suka hada da goyon bayan yaki da ta’addanci da Türkiye ke yi, tare da cire takunkuman da aka saka saboda ayyukan masana’antun tsaron Türkiye.
Daga cikin kasashe mambobin NATO, Türkiye da Hungary kadai ya ba su sanya hannu kan bukatar Swidin da Finland na shiga kawancen ba.