Manyan motocin tirela dauke da kayan taimako daga Kungiyar Bayar da Agaji ta Red Crescent ta Turkiyya sun fara shiga yankin gaza, bayan tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Kungiyar Gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas.
A ranar Juma'a kungiyar Red Crescent ta fara kai kayan taimako Gaza ta Kofar Iyaka ta Rafah, in ji wata sanarwa da kungiyar ta fitar.
Tare da hadin gwiwar da kungiyar Red Crescent ta Masar, sama da motocin tirela 30 ne suka shiga da kayan taimako, in ji sanarwar.
Kungiyar ta Red Crescent ta Turkiyya ta kuma ce ana ci gaba da ayyuka a dakunan girki, ind aake hidimtaw amutane 10,000 a arewacin Gaza da 15,000 a kudancin yankin. Tare da sabon tallafin, kungiyar tallarin ta Turkiyya na son kara adadin.
Taimakon da Kungiyar Agaji ta Masar ta taimaka wajen kai shi, na da manufar kai kayan taimakon cikin sauri zuwa Gaza tare da rabawa mabukata.
Kungiyar Red Crescent ta Turkiyya ta kudiri tallafa wa jama'ar yankin, inda ta ja hankali kan tarihin taimakon jin kai na shekaru 156 da suke bayarwa.
A ranar 19 ga Janairu, aka sanya hannu kan yarjejeniyar musayar fursunoni a Gaza, inda Isra'ila ta dakatar da kai hare-hare.
Tsagaita wutar da ke ci gaba da aiki, na cikin kashi na farko na kwanaki 42, wanda ya kunshi musayar fursunoni da yin sauran tattaunawa kan matakai na gaba.
Kusan Falasdinawa 47,000, mafi yawan su mata da yara kanana, sun rasa rayukansu, inda sama da 110,7000 suka jikkata sakamakon hare-haren Isra'ila a Gaza da ta fara kai wa tun 7 ga Oktoban 2023, kamar yadda ma'aikatan lafiya na yankin suka sanar.