Kilicdaroglu ne Jagoran ‘yan hamayyar Turkiyya/ Hoto: TRT World

Cikin sama da shekara 20, Kilicdaroglu ya yi suna a fagen siyasar Turkiyya a matsayin jagoran ‘yan hamayya.

Shugaban jam’iyyar CH, mai shekaru 74, ya kasance a siyasar Turkiyya tun 2002.

Amma ya gaza kayar da Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan da jam’iyyarsa ta AKP a lokutan zabuka.

Da farko sunansa Karabulut amma daga bisani mahaifinsa ya sauya masa suna zuwa Kilicdaroglu. An haife shi a lardin Tunceli ranar 17 ga Disamban 1948. Shi ne na hudu daga cikin yara bakwai da iyayensa suka haifa.

Bayan ya kammala digirinsa na farko a fannin Tsimi da Tanadi a Jami’ar Gazi a 1971, ya zama karamin akawu a ma’aikatar kudi ta Turkiyya.

Daga baya aka kara masa matsayi zuwa Akawu inda ya je Faransa tare da karo ilimi. Ya rike mukamai da yawa ciki har da na mukaddashin daraktan sashen tattara kudaden haraji a wannan ma’aikata.

Kafin ya tsunduma siyasa, Kilicdaroglu ya shugabanci Hukumar Kula da Inshora ta Turkiyya daga 1992 zuwa 1996.

A tsakanin 1997 da 1990 an sake zabar sa a matsayin Shugaban Hukumar Inshorar ta SSK.

Tsunduma harkokin siyasa

A 1999 Kilicdaroglu ya so ya samu takara a karkashin jam’iyyar DSP, karkashin tsohon Firaminista Bulent Ecevit, amma hakan bai yiwu ba.

A wannan lokacin ne shugaban jam’iyyar CHP Deniz Baykal ya bayar da babban taimako ga kilicdaroglu, ya gayyace shi don shiga jam’yyarsa. Ashe Baykal bai sani ba yana kokarin gina wanda zai gaji kujerar da yake kai ne.

A lokacin da yake majalisa, Kilicdaroglu ya fara tunkarar hanyar shugabantar CHP bayan Baykal ya yi murabus a 2010.

An fara zabar Kilicdaroglu zuwa majalisa a 2002 karkashin jam’iyyar CHP inda ya wakilci Istanbul har zuwa 2015.

Bayan sake zabar sa a matsayin dan majalisa a 2007, Kilicdaroglu ya rike mataimakin kakakin jam’iyyar CHP a majalisar dokoki.

A 2009, ya tsaya takarar magajin garin Istanbul karkashin jam’iyyar CHP, amma dan takarar AKP Kadir Topbas ya kayar da shi. Ya samu kaso 37 inda Topbas ya samu kaso 44.71 na jumullar kuri’un da aka jefa.

Shekara guda bayan an kayar da shi a zabe a Istanbul, Kilicdaroglu ya tsaya takarar shugabancin CHP saboda murabus din da Baykal ya yi sakamakon wani bidiyon abin kunya da ya faru.

A gajeren bidiyon da aka fitar, an ga Baykal na tara wa da mataimakiyar shugaban jam’iyya wadda kuma tsohuwar sakatariyarsa ce.

Duk da musanta wannan zargi tare da bayyana akwai masu yi masa tuggu, Baykal ya sauka daga kan kujerarsa, kuma Kilicdaroglu ya samu goyon bayan shugabannin larduna 77 inda ya zama sabon shugaban jam’iyyar adawa ta CHP.

A babban taron jam’iyyar na watan Mayun 2010, an zabi Kilicdaroglu a matsayin shugaban CHP.

A matsayin shugaban CHP, Kilicdaroglu ya zama shugaban jam’iyya ta biyu mafi yawan mambobi a Majalisar Dokokin Turkiyya.

Teburin ‘yan shida

Bayan samun nasarar shugabancin CHP a 2010, watanni kadan Kilicdaroglu ya dauki bangare a kuri’ar jin ra’ayin jama’a game da gyaran kundin tsarin mulki da aka yi a ranar 12 ga Satumban 201,0 inda ya yi gangamin neman kar a amince da bukatar sauye-sauyen da jam’iyyar AKP mai mulki ta kawo.

Ya yi kokarin kalubalantar kudirin sauye-sauyen da aka kawo amma Kotun Koli ta yi watsi da bukatarsa, kuma kaso 58 na jama’ar Turkiyya suka ce ‘e’ yayin da kaso 42 kuma suka ce ‘a’a’.

A shekarar da ta biyo baya, Kilicdaroglu ya shiga babban zaben 2011 a matsayin shugaban jam’iyyar CHP.

Jam’iyyar ta samu kaso 25.98 na kuri’un da aka jefa wanda ya ba su kujeru 135 a Majalisar Dokoki, inda AKP kuma ta samu kaso 49.83, sai MHP da ta samu kaso 13.01.

A wannan karon Kilicdaroglu ya zama dan majalisa daga mazabar Izmir har zuwa 2015.

A babban zaben 2015 kuma Kilicdaroglu ya samu kaso 24.95 na kuri’un da aka jefa inda ya tashi da adadin kujeru 132 a majalisar dokoki, kasa da yadda ya samu a zaben 2011.

A zabukan 2018, Kilicdaroglu ya kafa kawancen kasa tare da jam’iyyun adawa na a IYI karkashin Meral Aksener, Temel Karamollaoglu na Jam’iyyar Saadet da Gultekin Uysal na Jam’yyar DP.

Kawancen Kasa na Kilicdaroglu ya sake fadada a watan Fabrairun 2022: shugabannin jam’iyyun adawa shida tare da Ahmet Davutoglu na jam’iyyar Gelecek da Ali Babacan na jam’iyyar DEVA sun shiga kawancen.

Daga nan suka sa wa kansu sunan ‘Teburin ‘yan shida’.

A yanzu da jam’iyyu biyar suke mara wa Kilicdaroglu baya a kokarinsa na zama shugaban Turkiyya.

Shin zai yi nasara a wannan karon ko Shugaba Erdogan zai sake yin nasara a kansa?

TRT World