Sakamakon karshe na fitowa a yayin da aka kidaya fiye da kashi 96 na zaben shugaban kasar Turkiyya. Kawo yanzu Shugaba Erdogan ya samu kashi 49.34 yayin da babban dan hamayya Kilicdaroglu ya samu kashi 45.00.
An soma jefa kuri’a da misalin 8:00 na safe (05:00 GMT) inda kuma aka rufe rumfunan zabe da misalin 5:00 na yamma (14:00 GMT).
An haramta wa kafafen watsa labarai bayyana sakamakon zaben wucin-gadi har sai karfe 9:00 na dare (18:00 GMT).
Idan babu dan takarar da ya samu sama da rabin kuri’un da aka jefa a zagayen farko na zaben, za a gudanar da zagaye na biyu a ranar 28 ga watan Mayu. Akwatunan zabe 191,885 aka tanadar a kasar domin jefa kuri’ar.
Akwai jam’iyyun kawance da suke takara: sun hada da the People's Alliance, Nation Alliance, Ata Alliance, Labour and Freedom Alliance, da Union of Socialist Alliance.
Bayanai na baya-bayan nan
1241 GMT — Za a je zagaye na biyu na zaben shugaban kasa, a cewar hukumar koli ta zabe YSK
Shugaban Hukumar Koli ta Zabe a Turkiyya YSK, Ahmet Yener ya sanar da cewa za a yi zabe zagaye na biyu ranar 28 ga watan Mayu saboda babu dan takarar da ya samu kashi 50 cikin 100 na jumullar kuri'un da aka kada a zagaye na farko.
"Jumullar kuri'un da aka kada a zabuka a fadin kasar sun nuna kashi 88.92 cikin yawan masu zabe da suka yi rajista ne suka kada kuri'a, yayin da kashi 52.69 ne yawan wadanda suka kada kuri'a daga kasashen waje cikin masu rajista," in ji shi.
0345 GMT — An kirga kashi 98.55 na kuri'un sakamakon zaben shugaban kasa na baya-bayan nan
• Erdogan: ya samu kashi 49.34
• Ince: ya samu kashi 0.43 (ya janye)
• Kilicdaroglu: ya samu kashi 45.00
• Ogan: ya samu kashi 5.23
0155 GMT — An kirga kashi 98.06 na kuri'un sakamakon zaben shugaban kasa na baya-bayan nan
• Erdogan: ya samu kashi 49.34
• Ince: ya samu kashi 0.43 (ya janye)
• Kilicdaroglu: ya samu kashi 44.99
• Ogan: ya samu kashi 5.24
0150 GMT — Sakamakon zaben majalisar dokoki na baya-bayan nan
Sakamakon zaben shugaban kasa na baya-bayan nan inda aka kirga kashi 97.23:
• Kawancen Al'umma: ya samu kashi 49.30
• Kawancen 'Yan Kasa: ya samu kashi 35.22
0122 GMT — Zabe ya bayyana me jama'ar kasa ke so: Ofishin Daraktan Sadarwa
Zabukan shugaban kasa da na 'yan majalisar dokokin Turkiyya sun sake bayyana me jama'ar kasar ke so, inji Daraktan Sadarwa na Turkiyya.
Ranar 14 ga Mayu ta sake zama rana da aka sake bayyana 'abun da kasar nan mai daraja ke so", inji Fahrettin Altun a wani sako da ya fitar ta shafin Twitter.
Altun ya rubuta "Kasarmu ta yi magana tare da nuna hanyar da za a bi. Ta hanyar nuna goyon baya da zama lafiya za mu zama abun misali ga duniya."
2355 GMT — An kirga kashi 97.23 na kuri'un sakamakon zaben shugaban kasa na baya-bayan nan
• Erdogan: ya samu kashi 49.36
• Ince: ya samu kashi 0.44 (ya janye)
• Kilicdaroglu: ya samu kashi 44.96
• Ogan: ya samu kashi 5.25
2313 GMT — Mun yi tazara sosai a zabukan da aka gudanar: Erdogan
Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ce ya "samu tazara mai yawa" a zaben shugaban kasar da aka gudanar.
A yayin da yake jawabi ga magoya bayansa a hedikwatar jam'iyyarsa ta AK Party a Ankara, ya ce har yanzu ana cigaba da kirga kuri'un da aka kada a kasar da wadanda aka jefa a kasashen waje, yana mai karawa da cewa kwarywa-kwaryar sakmako ya nuna cewa "muna kan gaba da tazara mai yawa sosai."
Ya ce ya samu tazarar fiye da kuri'a miliyan 2.6 a kan hamayyar da yake biye masa na kurkusa, yana mai cewa adadin zai karu idan aka kammala fitar da sakamakon zaben.
Shugaba Edogan ya ce kasar ta kammala wani "biki na dimokuradiyya" a zaben 14 ga watan Mayu, inda yakara da cewa adadin wadanda suka fiti kada kuri;afrsu ya zarta na kowane lokaci a tarihin kasar.
2250 GMT — An kirga kashi 96.15 na kuri'un sakamakon zaben shugaban kasa na baya-bayan nan
• Erdogan: ya samu kashi 49.44
• Ince: ya samu kashi 0.44 (ya janye)
• Kilicdaroglu: ya samu kashi 44.86
• Ogan: ya samu kashi 5.26
2205 GMT — An kirga kashi 95.09 na kuri'un sakamakon zaben shugaban kasa na baya-bayan nan
• Erdogan: ya samu kashi 49.52
• Ince: ya samu kashi 0.44 (ya janye)
• Kilicdaroglu: ya samu kashi 44.76
• Ogan: ya samu kashi 5.28
2135 GMT — An kirga kashi 94.24 na kuri'un sakamakon zaben shugaban kasa na baya-bayan nan
• Erdogan: ya samu kashi 49.59
• Ince: ya samu kashi 0.45 (ya janye)
• Kilicdaroglu: ya samu kashi 44.67
• Ogan: ya samu kashi 5.29
2030 GMT — Dole kowa ya girmama zabin jama'a: Kakakin jam'yyar AKP
Kakakin jam'iyyar AKP Omer Celik ya sanar da cewa wajibi ne a kan kowa ya girmama zabin jama'ar Turkiyya da kuma kwarewar dabbaka dimukradiyya da suka nuna.
"Arziki mafi girma da kasar nan ke da shi, shi ne yadda jama'a da kansu suke zabar wanda zai jagoranci wannan kasa."
2030 GMT — An kirga kashi 92.7 na kuri'un sakamakon zaben shugaban kasa na baya-bayan nan
• Erdogan: ya samu kashi 49.94
• Ince: ya samu kashi 0.46 (ya janye)
• Kilicdaroglu: ya samu kashi 44.30
• Ogan: ya samu kashi 5.30
2030 GMT — An kirga kashi 87.7 na kuri'un sakamakon zaben shugaban kasa na baya-bayan nan
• Erdogan: ya samu kashi 50.20
• Ince: ya samu kashi 0.48 (ya janye)
• Kilicdaroglu: ya samu kashi 44.02
• Ogan: ya samu kashi 5.30
2030 GMT — An kirga kashi 75.25 na kuri'un sakamakon zaben majalisar dokoki na baya-bayan nan
• Kawancen Al'umma: kashi 50.99
• Kawancen 'Yan Kasa: kashi 34.25
2015 GMT — An kirga kashi 82.54 na kuri'un sakamakon zaben shugaban kasa na baya-bayan nan
• Erdogan: ya samu kashi 50.30
• Ince: ya samu kashi 0.48 (ya janye)
• Kilicdaroglu: ya samu kashi 43.91
• Ogan: ya samu kashi 5.31
2010 GMT — Erdogan ya wallafa sako a Twitter "yana yabon tsarin dimokradiyyar Turkiyya"
Shugaba Erdogan ya wallafa sako a Twitter yana mai cewa an yi zaben "cikin sauki" kuma hakan ya nuna kyawun tsarin dimokradiyyar Turkiyya.
"A yayin da aka kammala kada kuri'a a yanayin mai kyau na dimokradiyya, gaggawar sanar da sakamakon a yayin da ake ci gaba da kirga kuri'u zai iya kawo matsala ga tsarin kasar," in ji Erdogan.
"Muna jin dadin ganin yadda ake ci gaba da kirga kuri'un bisa tsarin da mutane ke so. Ina kira ga dukkan abokan aikina da abokan arziki da cewa kar su bar wajen akwatunan zaben har sai an kammala fitar da sakamako a hukumance, duk irin abin da zai faru," ya kara da cewa.
2000 GMT — An kirga kashi 79.45 na kuri'un sakamakon zaben shugaban kasa na baya-bayan nan
• Erdogan: 50.50 percent
• Ince: 0.49 percent (withdrawn)
• Kilicdaroglu: 43.70 percent
• Ogan: 5.31 percent
1945 GMT — An kirga kashi 75.79 na kuri'un sakamakon zaben shugaban kasa na baya-bayan nan
• Erdogan: ya samu kashi 50.76
• Ince: ya samu kashi 0.50 (ya janye)
• Kilicdaroglu: ya samu kashi 43.43
• Ogan: ya samu kashi 5.31
1945 GMT — An kirga kashi 62.23 na kuri'un sakamakon zaben majalisar dokoki na baya-bayan nan
• Kawancen Al'umma: kashi 52.09 cikin 100
• Kawancen 'Yan Kasa: kashi 33.44
1930 GMT — An kirga kashi 74.9 na kuri'un sakamakon zaben shugaban kasa na baya-bayan nan
• Erdogan: ya samu kashi 50.97
• Ince: ya samu kashi 0.50 (ya janye)
• Kilicdaroglu: ya samu kashi 43.22
• Ogan: ya samu kashi 5.31
1915 GMT — An kirga kashi 70.4 na kuri'un sakamakon zaben shugaban kasa na baya-bayan nan
• Erdogan: ya samu kashi 51.23
• Ince: ya samu kashi 0.51 (ya janye)
• Kilicdaroglu: ya samu 42.95
• Ogan: ya samu kashi 5.31
1915 GMT — An kirga kashi 49.85 na kuri'un sakamakon zaben shugaban kasa na baya-bayan nan
• Kawancen Al'umma: kashi 53.25
• Kawancen 'Yan Kasa: kashi 32.59
1900 GMT — An kirga kashi 65.7 na kuri'un sakamakon zaben shugaban kasa na baya-bayan nan
• Erdogan: ya samu kashi 51.44
• Ince: ya samu kashi 0.51 (ya janye)
• Kilicdaroglu: ya samu kashi 42.73
• Ogan: ya samu kashi 5.32
1845 GMT — An kirga kashi 60.4 na kuri'un sakamakon zaben shugaban kasa na baya-bayan nan
• Erdogan: ya samu kashi 51.71
• Ince: ya amu kashi 0.52 (ya janye)
• Kilicdaroglu: ya samu kashi 42.45
• Ogan: ya samu kashi 5.32
1815 GMT — An kirga kashi 47.55 na kuri'un sakamakon zaben shugaban kasa na baya-bayan nan
• Erdogan: ya samu kashi 52.2
• Ince: ya samu kashi 0.5 (ya janye)
• Kilicdaroglu: ya samu kashi 41.9
• Ogan: ya samu kashi 5.3
1800 GMT — An kirga kashi 43.7 na kuri'un sakamakon zaben shugaban kasa na baya-bayan nan
• Erdogan: ya samu kashi 52.6
• Ince: ya samu kashi 0.5 (ya janye)
• Kilicdaroglu: ya samu kashi 41.6
• Ogan: ya samu kashi 5.4
1745 GMT — An kirga kashi 37.9 na kuri'un sakamakon zaben shugaban kasa na baya-bayan nan
• Erdogan: ya samu kashi 53.02
• Ince: ya samu kashi 0.56 (ya janye)
• Kilicdaroglu: ya samu kashi 41.04
• Ogan: ya samu kashi 5.38
1745 GMT — Sakamakon zaben majalisar dokoki na baya-bayan nan
Ana ci gaba da kada kuri'un majalisar dokokin Turkiyya. Ga sabbin alkaluman sakamakon bayan kirga kashi 13.19 cikin 100:
• Kawancen Al'umma: kashi 60.19
• Kawancen 'Yan Kasa: kashi 26.78
1730 GMT — Sakamakon baya-bayan nan sun nuna an kirga kashi 31.5 cikin 100 na kuri'un
• Erdogan: ya samu kashi 53.62
• Ince: ya samu kashi 0.56 (ya janye)
• Kilicdaroglu: ya samu kashi 40.42
• Ogan: ya samu kashi 5.40
1715 GMT — Erdogan na kan gaba a sakamakon farko da ya fara fitowa
Sakamakon farko-farko sun fara zuwa, inda aka kirga kashi 24.7 cikin 100 na kuri'un.
• Erdogan: yana da kashi 54.63
• Ince: yana da kashi 0.56 (ya janye)
• Kilicdaroglu: yana da kashi 39.40
• Ogan: yana da kashi 5.41
1635 GMT— An dage haramcin da aka sanya da watsa labaran sakamakon zabe
Hukumar Koli ta Zabe ta Turkiyya (YSK) ta dage haramcin da aka sanya wa kafafen watsa labarai na sanar da sakamakon zabe da misalin karfe 6:30 na yamma agogon kasar, wato 5.30 agogon GMT, kamar yadda shugaban hukumar YSK, Ahmet Yener ya shaida wa manema labarai a Ankara, babban birnin kasar.
1500 GMT — An kammala zabe, an soma kirga kuri'a
An rufe rumfunan zabe sannan an soma kirga kuri'u a zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokokin Turkiya.
1145 GMT - Ana sa ran masu kada kuri'ar za su zarta kashi 90 cikin dari
Wakilin TRT World Mustafa Fatih Yavuz da ke Ankara ya ce an yi fitar-dango wurin kada kuri'a a Ankara da ma a fadin Turkiyya.
A 1987 adadin masu kada kuri'a ya kai kashi 93.3 yayin da a 2018 ya kai 86.2.
Yavuz ya ce ana sa ran adadin masu kada kuri'a a wannan shekarar zai zarta kashi 90.
Kazalika adadin masu kada kuri'a a kasashen waje ya karu daga kashi 50 a 2018 zuwa kashi 53 a wannan shekarar.
1130 GMT - Mace mai shekara 112 ta jefa kuri'arta
Gullu Dogan, mace mafi tsufa a Gumushane, mai shekara 112, ta yi kokari ta kada kuri'arta tare da 'ya'yanta da jikokinta a wata mazaba.
Duk da yake tana da zabin jefa kuri'a ta hanyar akwatunan zabe na tafi-da-gidanka, matar ta zabi zuwa rumfar zabe don kada kuri'a.
0830 GMT- Shugaban Turkiyya ya jefa kuri’a
Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya jefa kuri’a a zaben shugaban kasar da na ‘yan majalisa. “An ci gaba da jefa kuri’a a kasar ba tare da wata matsala ba.
‘Yan kasarmu da ke yankin da girgizar kasa ta rutsa da su suna zabe cikin karsashi. Ba mu fuskanci wata matsala a yankin ba,” kamar yadda Erdogan ya shaida wa manema labarai a lokacin da yake jefa kuri’arsa a gundumar Uskudar da ke Santambul.
Ya yi addu’a “kasar da siyasar kasar su samu makoma ta gari”.
0800 GMT – Dan takarar jam’iyyar adawa Kılıçdaroğlu ya jefa kuri’a
Shugaban Jam’iyyar Republican People’s Party (CHP) kuma dan takarar shugaban kasa Kemal Kılıçdaroğlu ya jefa kuri’a a zaben kasar. Kılıçdaroğlu ya jefa kuri’arsa a makarantar Arjantin da ke Ankara.
0500GMT – An fara zaben shugaban kasa da na 'yan majalisa a Turkiyya
An soma zabe a fadin Turkiyya a ranar Lahadi a zaben shugaban kasa da kuma ‘yan majalisar kasar.
Shugaba mai ci Recep Tayyib Erdogan na neman wani wa’adi inda ‘yan takarar jam’iyyun adawa Kemal Kilicdaroglu na Nation’s Alliance da kuma Sinan Ogan ke fafatawa da shi.
Hukumar zaben Turkiyya YSK ta sanar da cewa sama da ’yan kasar miliyan 64 suka cancanta su yi zabe a ranar 14 ga watan Mayu, ciki har da sama da mutum miliyan uku da ke zaune a kasar waje.
Za a rufe zaben da misalin karfe 5:00 agogon kasar kuma ana sa ran sakamakon farko-farko za su fara fitowa.