Yahudawa 'yan kama guri zauna da 'yan sandan Isra'ila na yawan kai wa Musulmai hari a Masallacin Aksa / Hoto: AA

Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi suka da babbar murya kan harin da Isra’la ta kai wa Masallacin Kudus a yankin Gabashin Birnin Kudus da Yahudawa suka mamaye, yana mai cewa, “Ina son bayyana bakin ciki da bacin raina”.

“Turkiyya ba za ta taba yin shiru ba idan aka kai irin wannan hari. A je Masallacin Kudus a ci zarafin Haramin Alsharif, wannan keta jan layinmu ne”, in ji Shugaba Erdogan.

Ya yi wadannan kalamai ne a wani taron buda bakin azumi da ya yi da tsofaffin ma’aikata a Ankara, babban birnin kasar

Erdogan ya mayar da wannan martani ne bayan da ‘yan sandan Isra’ila suka kai hari kan Musulmai da ke Ibada kusan su 350 a cikin Masallacin na Kudus.

Rikicin ya faru ne a lokacin da wasu Yahudawa ‘yan kama guri zauna suka kira jami’an tsaron Isra’la kan su zo su tayar da zaune tsaye a Masallacin Aksa a lokacin da Musulmai ke Sallar Asham.

Matasan Musulman sun rufe kofofin masallacin don kare kawunansu daga ‘yan sandan Isra’ila.

'Yan sandan sun yi amfani da bama-bamai masu kara, inda suka karya wunduna don samun damar shiga masallacin.

Erdogan ya ce Isra’ila na bin “salon siyasar zalunci”, kuma Falasdinawa ba su kadai ba ne a wannan gwagwarmaya da suke yi.

TRT World