Jami'an Turkiyya sun 'kawar' da shugaban YPG/PKK a Syria

Jami'an Turkiyya sun 'kawar' da shugaban YPG/PKK a Syria

Mehmet Sari yana da hannu a ayyukan ta'addanci da dama a Turkiyya da Syria.
Mehmet ya gudu Syria a 2014 bayan ya kai jerin hare-haren ta'addanci a Turkiyya. Photo/A

Jami’an leken asirin Turkiyya sun “kawar da” wani babban dan ta’adda na kungiyar YPG/PKK a arewacin Syria.

Mehmet Sari, wanda aka fi sani da Baran Kurtay, ya gamu da gamonsa ne a wani samame na dakile harin ta’addanci da aka kai a lardin Qamishli na Syria ranar 14 ga watan Afrilu, kamar yadda majiyoyin tsaro suka bayyana a ranar Talata.

Mehmet ya gudu Syria ne a 2014 bayan ayyukan ta’addanci a Turkiyya.

Sari, wanda shi ne shugaban YPG da PKK a yankin Raqqa, yana da alaka da shugabancin PKK.

Yana da hannu a ayyukan ta’addanci a Raqqa da ke arewa maso tsakiyar Syria.

Hukumomin Turkiyya sun yi amfani da “kawarwa” domin nuna cewa dan ta’addan ko dai ya mika kansa ko an kashe shi ko an kama shi.

Turkiyya da Amurka da Tarayyar Turai sun ayyana PKK a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda – kuma ta jawo mutuwar sama da mutum 40,000 ciki har da mata da kananan yara.

AA