Dakarun Turkiyya sun yi nasarar kame wani jigon ƙungiyar ta'addanci ta PKK, a wani farmakin haɗin gwiwa da hukumar leƙen asiri ta ƙasa (MIT) da ƴan sanda suka kai.
Hukumar ta MIT ta yi nasarar gano inda ɗan ta'addan nan Murat Kizil yake, wanda ke ɓoye a ƙasashen waje da sunan "Mazlum Mardin," a lokacin da yake yunƙurin tserewa zuwa Turai.
An samu rahoton cewa Kizil ɗan ta'addan da aka kama wanda aka kawo ƙasar Turkiyya ya shiga cikin ƴan ta'addar PKK/KCK na ƙungiyar ta'addanci ta PKK a shekarar 2015.
An ba da rahoton cewa Kizil, wanda ya yi aiki a matakin da ke da alhakin kai hare-hare a Siriya da Iraƙi, "mamba ne a ƙungiyar ta'addanci."
Yaƙin da Turkiyya ke yi da PKK
Ma'aikatar Tsaron Turkiyya ta sanar a ranar Alhamis cewa, Turkiyya ta kawar da ƴan ta'adda 60 a cikin makon da ya gabata, ciki har da waɗanda ke ɓoye a kan iyakar Iraƙi da Siriya.
Kakakin ma'aikatar harkokin cikin gida na Turkiyya Zeki Akturk, ya shaid wa maneman labarai cewa an kawar da ƴan ta'adda 458 a hare-haren da ake kai wa dukkanin ƙungiyoyin ƴan ta'adda, musamman PKK/PYD-YPG da Daesh da FETO, tare da 184 a arewacin Iraƙi da kuma 274 arewacin Siriya tun daga 1 ga watan Janairun 2024.
Ya ce an kashe ƴan ta'adda 824 a cikin Operation Claw-Lock ya zuwa yanzu, wanda aka ƙaddamar a watan Afrilun 2022 don kai hari kan maɓoyar ƙungiyar ta'adda ta PKK a Metina da ke arewacin Iraƙi da Zap da Avasin-Basyan da ke kusa da iyakar Turkiyya.
Ya ƙara da cewa "Za a ci gaba da aiwatar da yyyukan yaƙi da ta'addanci na Ankara a cikin azama."
Mahukuntan Turkiyya na amfani da kalmar "kawarwa" don nuna cewa ƴan ta'addan da ake magana sun miƙa wuya ko an kashe su ko kuma aka kama su.
A cikin sama da shekaru 35 da take yi na ta'addanci a kan Turkiyya, PKK - wadda Turkiyya da Amurka da EU suka ayyana a matsayin ƙungiyar ta'addanci - ta ɗauki alhakin mutuwar mutum fiye da 40,000 da suka haɗa da mata da yara da jarirai. YPG reshen ƙungiyar ta'addanci ta PKK ne a Siriya.