Shugabannin Turkiyya da ministoci ciki har da shugaban kasar Recep Tayyip Erdogan sun yi murnar cikar kasar shekara 100 da zama Jamhuriya.
“Muna cikin farin ciki da alfahari game da cika shekaru 100 da kafuwar Jamhuriyarmu a yau. Ina taya 'yan kasarmu da ke zaune a kasarmu da ma duniya baki daya murnar ranar Jamhuriya ta 29 ga Oktoba," in ji Erdogan a sakon da ya wallafa a shafin X.
Erdogan da sauran manyan kasar daga baya sun kai ziyara Anitkabir, inda aka binne Mustafa Kemal Ataturk, wanda ya kirkiro sabuwar Turkiyya.
“Mun yi kokarin kare abin da ka bar mana yadda ya kamata a tsawon shekaru 21 na gwamnatinmu, inda kowane lokaci da muka shafe kasarmu muke yi wa aiki,” kamar yadda ya rubuta a littafin baki na Anitkabir.
"A matsayinmu na gwamnatin da ta hada Turkiyya tare da kawo hanyoyin zuba jari a tarihi, mun kudiri aniyar shiga karni na biyu na Jahuriyarmu da karni na farko na Turkiyya.
Jamhuriyarmu tana da aminci fiye da kowane lokaci kuma tana cikin aminci a hannun kwararru."
Allah Ja zamanin Karnin Turkiyya
Kakakin Majalisa Numan Kurtulmus ya bayyana cewa Turkiyya na “yunƙurin cika shekara 100 tare da kalmomi masu ƙarfi da ayyuka masu inganci, daidai da imani da ƙoƙarin da al'ummarmu masu ƙauna suka nuna."
Shi ma daraktan watsa labarai na Turkiyya Fahrettin Altun shi ma ya yi murna ga Turkiyya a daidai lokacin da kasar ta cika shekara 100 da zama jamhuriya: “Ina fata Turkiyya wadda nake jin dadin kasancewa a cikinta, ta kasance har abada.”
“A daidai wannan lokacin, ina tunawa cikin rahama ga dukkan shahidanmu wadanda suka sadaukar da rayukansu ga kasarmu, musamman wanda ya kirkiro sabuwar Jamhuriyarmu, Gazi Mustafa Kemal Ataturk.
Allah Ja zamanin wannan Jamhuriyar, Allah Ja Zamanin shekara 100 na Turkiya,” kamar yadda ya bayyana.
“Tun daga kirkiro jamhuriyar zuwa yanzu, karkashin tutarmu mai rabin wata, mun fahimci cewa sadaukar da komai domin rayuwa a matsayin kasa daya, mun kuma rike dimokuradiyya.”
“Za mu ci gaba da ji da kuma kiyaye kanmu,” kamar yadda mataimakin shugaban kasa Cevdet Yilmaz ya bayyana. Shi ma Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya ce “ za mu ci gaba da daukar matakai da don samun ingantacciyar duniya a matsayin alama ta zaman lafiya, hankali, adalci, da amana."
Ministan tsaro Yasar Guler ya bayyana cewa “Muna matukar farin ciki da cika shekara 100 da zama Jamhuriya, wadda aka kaddamar bayan yakin neman ‘yancin kan Turkiyya karkashin Gazi Mustafa Kemal Ataturk, da nuna jarumtaka da sadaukar da kai domin kare kasarmu da tutarmu da ‘yancinmu,” in ji ministan.
Ma’aikatar Tsaro a sako na daban da ta aika ta ce: “Mua murnar cika shekara 100 da samun ‘yanci! Muna tunawa da godiya ga wanda ya kirkiro Jamhuriya, da Babban Kwamanda, Gazi Mustafa Kemal Ataturk, da kuma sauran jaruman yakin neman ‘yancin kan Turkiyya.
“Za mu ci gaba da aiki da duka karfinmu domin kaiwa ga matakin ci gaba da Ataturk ya nuna, da kuma tsayuwar Turkiyya a matsayin kasa daya a karnin da mutum miliyan 85.”