Hukumar Leken Asiri ta Turkiyya MIT ta kawar da babban dan ta'adda na kungiyar PKK/KCK da ke horar da al'umma kan ayyukan ta'addanci a yankin kauyen Hakurk na kasar Iraki.
MIT ta yi nasarar kawar da dan ta'addan mai suna Rozerin Semzinan da aka fi sani da Sariye Atilla yayin da yake gudanar da wani aiki a kauyen Hakurk.
Semzinan da ya shiga kungiyar ta'addancin ne a shekarar 2007, kazalika rahotannin sun yi nuni da cewa malami ne dake karantarwa a wuraren horar da yan'taddan PKK a yankin Haftanin, a baya- bayan nan ne ya shiga harkokin da suka shafi zamantakewar al'umma a Hakurk, a cewar MIT.
Hukumar MIT ta Turkiyya ta ce sai da ta bi diddigin dukkan bayanan da ta samu daga jami'anta na kasa inda ta gano inda dan' ta'addan ya ke, kana ta sanya ido akansa sosai har ta kai ga kawar da shi a daidai yanayin da ya dace.
MIT da ke ci gaba da kai hari kan kungiyoyin 'yan ta'adda a kowane fanni, ta isar da wani sako bayan nasarar da ta samu a aikinta na baya-bayan nan, na ci-gaba da gudanar da ayyukanta kai tsaye a maɓoyar 'yan ta'adda a matsayin wani bangare a manufofinta na kawar da ayyukan ta'addanci da masu mara musu baya a nan gaba.
Mahukuntan Turkiyya na amfani da kalmar ''kawarwa'' ga 'yan ta'addan da suka miƙa wuya ko aka kashe su ko kuma aka kama su.
A shekaru sama da 35 a ayyukanta na ta'addancin a kan Turkiyya, kungiyar PKK - wadda kasar Turkiyya da Amurka da kungiyar Tarayyar Turai EU suka sanya a matsayin kungiyar ta'addanci - ta dauki alhakin mutuwar sama da mutum 40,000, ciki har da mata da yara da kuma jarirai.