Hukumar Leken Asiri ta Turkiyya MIT ta yi nasarar kawar da wasu 'yan ta'addar ƙungiyar PKK/KCK guda biyu da suka yi shirin kai hari kan dakarun ƙasar.
Hukumar MIT ta bankaɗo cewa, manyan jagororin ƙungiyar PKK sun bai wa Vesile Duran da aka fi sani da Ronahi Dilhvin da kuma Dilan Oklu da aka fi sani da Arin Tolhildan waɗanda ake nema ruwa a jallo umarnin shirya kai hari a yankin da jami'an tsaron Turkiyya suke gudanar da ayyukansu a Hakurk na ƙasar Iraki, a cewar majiyoyin tsaro.
Bayan bayanan sirri da hukumar MIT ta samu, ya ba ta ƙarfin gwiwar bin diddigin ayyuka da kuma shirye-shiryen Duran da Oklu, har zuwa lokacin da 'yan ta'addar suka isa wurin da suka shirya kai harin, anan ne MIT ta kaddamar da wani hari da ta shirya wanda ya yi sanadin kawar da 'yan ta'addan biyu.
Vesile Duran, wacce aka fi sani da Ronahi Dilhvin, ta shiga kungiyar ta'adda ta PKK/KCK ne a shekarar 2014, sannan ta koma arewacin Iraki a shekarar 2015, inda ta samu horon soji da kuma akidar ƙungiyar. Ta kasance a yankin Hakurk har zuwa lokacin.
Dilan Oklu, wadda aka fi saninta da Arin Tolhildan, 'yan ta'addar PKK ne suka ɗauke ta aiki a shekarar 2014 a lokacin tana 'yar shekara 15.
Ta samu horo na dole kan ayyukan soji da kuma sanin aƙidar ƙungiyar a arewacin Iraki.
Oklu 'yar'uwa ce ga Vedat Oklu, wadda aka fi sani da Tolhildan Zevki, wata 'yar ta'addar PKK da aka kashe a shekarar 2019. Ta kasance mai fafutuka a yankin Hakurk.