Ministan tsaron kasar Turkiyya ya bayyana cewa an kashe 'yan ta'addar PKK/YPG 77, an kuma lalata wurare 78 da suka hada da cibiyoyin mai da kungiyoyin 'yan ta'adda ke iko da su, da matsugunai, da koguna a hare-haren da aka kai ta sama a arewacin Iraki da Siriya.
“An lalata jimillar wurare 78 da suka hada da kogun da matsugunai da maboya, da wuraren mai da aka ayyana cewa kungiyoyin ‘yan ta’adda na ‘yan aware ne ke amfani da su, ta hanyar hare-haren sama da aka kai a yankunan Metina da Hakurk da Gara da Kandil a yankuna a arewacin Iraki, da kuma arewacin Siriya.
"An kuma kashe 'yan ta'adda 77," in ji Minista Yasar Guler a wani taro na intanet da ya yi tare da manyan kwamandojin sojojin Turkiyya a ranar Litinin.
"Wadannan ayyuka suna tabbatar da cewa jinin shahidanmu bai tafi a banza ba. Yakin da muke yi da ta'addanci zai ci gaba da tsananta har sai babu wani dan ta'adda da ya rage.
Ya kara da cewa, ko shakka babu za a ci gaba da aiwatar da wannan aiki da azama da himma, musamman kan kungiyoyin ta'addanci irinsu PKK, YPG, FETO, Daesh, da manufar kawar da ta'addanci daga tushensu.
Manyan kwamandojin sun hada da babban hafsan hafsoshin sojin kasar Janar Metin Gurak, da kwamandan sojojin ruwa Adm. Ercument Tatlioglu, da kwamandan sojojin kasa Janar Selcuk Bayraktaroglu, da kwamandan sojojin sama Janar Ziya Cemal Kadioglu.
Minista Guler, wanda ya samu bayani game da ayyukan da ake gudanarwa, musamman ayyukan yaki da ta'addanci, ya ba da umarni game da ayyukan da ke tafe.
Jami'an tsaro sun fara fatattakar 'yan ta'addar PKK/YPG, bayan kashe sojojin Turkiyya tara a ranar Juma'a a wani harin ta'addanci da aka kai a arewacin Iraki,
'Yan ta'addar PKK suna yawan fakewa a arewacin Iraki domin shirya kai hare-haren wuce gona da iri a Turkiyya. Har ila yau kungiyar tana da reshen Syria da aka fi sani da YPG.
A cikin sama da shekaru 35 da ta shafe tana ayyukan ta'addanci a kan Turkiyya, kungiyar ta'addar PKK - wacce Turkiyya da Amurka da Tarayyar Turai suka sanya a matsayin kungiyar 'yan ta'adda - ita ta yi sanadin mutuwar mutum fiye da 40,000 da suka hada da mata da yara da jarirai.