Turkiyya da Masar suna da buƙatu iri ɗaya kan lamuran da suka shafi Falasɗinawa, kuma dukkansu suna son ganin Isra'ila ta gaggauta daina kai hare-hare a Gaza, a cewar Shugaba Recep Tayyip Erdogan.
“Gudunmawar da Turkiyya da Masar suke bayarwa wajen zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin tana da matuƙar muhimmanci,” in ji Erdogan ranar Laraba, a yayin da yake gabatar da jawabi ga manema labarai tare da takwaransa na ƙasar Masar Abdel Fattah el Sisi, wanda ke ziyarar aiki a Turkiyya.
Wannan ce ziyarar aiki ta farko da Sisi ya kai Turkiyya tun da ya soma mulki a 2014. Ya kai ziyarar ce sakamakon gayyatar da Erdogan ya yi masa.
A wani ɓangare na ziyarar da Sisi yake yi, shugabannin biyu sun jagoranci wani Babban Taro Kan Haɗin-Kai tsakanin ƙasashen biyu tare da sanya hannu kan yarjeniyoyi 17 a fannoni daban-daban.
"Mun jaddada aniyarmu ta haɗin-kai a dukkan ɓangarori, ciki har da masana'antu da cinikayya da tsaro da kiwon lafiya da muhalli da makamashi,” a cewar Erdogan, wanda ya ƙara da cewa ƙasashen biyu za su kyautata alaƙa a tsakaninsu ta yadda kowane ɓangare zai "ci moriyarta.”
A nasa ɓangaren, Sisi ya ce ziyarar da ya kai Turkiyya "ta buɗe sabuwar hanya a fannin tattalin arziki da cinikayya,” sannan ya jaddada matsayin ƙasashen biyu game da “wajabcin tsagaita wuta a Gaza da kuma kawo ƙarshen hare-haren da Isra'ila take kai wa a Gabar Yammacin Kogin Jordan.”
Daɗaɗɗen tarihi na abota
Turkiyya da Masar, waɗanda suka kasance biyu daga cikin manyan ƙasashen Gabas ta Tsakiya, suna ci gaba da ƙarfafa alaƙar da ke tsakaninsu a wani ɓangare na shirin ƙara kusantar juna da suka ƙaddamar shekaru uku da suka gabata.
A watan Fabarairu, shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya kai ziyara Masar, inda ya gana da Sisi tare da sanya hannu kan yarjeniyoyi a fannin yawon buɗe ido da al'adu da ilimi.
Cinikayya ita ce maƙasudin ƙarfafa alaƙa a tsakanin Turkiyya da Masar. Ƙasashen biyu suna fatan ƙara cinikayya a tsakaninsu da aƙalla kashi 50, wato daga dala biliyan 10 zuwa dala biliyan 15.
Turkiyya na cikin manyan ƙasashen da suka fi gudanar da harkokin kasuwanci da Masar a shekaru 10 da suka gabata.
Ƙasashen biyu suna da daɗaɗɗen tarihi na abota. A shekara mai zuwa ne Turkiyya da Masar za su cika shekara 100 da ƙulla dangantakar diflomasiyya.
Sanarwar haɗin-gwiwa
A sanarwar haɗin-gwiwar da Turkiyya da Masar suka fitar bayan kammala Babban Taro Kan Haɗin-Kai a tsakaninsu, Ankara da Kairo sun jaddada haɗin gwiwarsu wajen goyon bayan Falasɗinu da kawo ƙarshen hare-haren da Isra'ila take kai wa Gaza.
Ƙasashen biyu sun ce Falasɗinawa suna da 'yancin samun ƙasa mai cin gashin kanta, wadda Gabashin Birnin Ƙudus zai kasance babban birninta, bisa iyakokin da aka shata a 1967. Kazalika sun jaddada matsayarsu ta kare 'yancin Falasɗinawa da aka kora daga gidajensu.
Haka kuma sun jaddada goyon bayan Iraƙi a matsayin ƙasa mai 'yancin kansa da ke neman zaman lafiya, tare da goyon bayan ci gaban Iraƙi da yunƙurin sake gina ta.
Kazalika Turkiyya da Masar sun jaddada goyon bayansu ga tsarin siyasar al'ummar Libya kamar yadda MDD take yi, wada zai kasance mataki na tabbatar da zaman lafiya da tsaro da haɗin-kai na Libya.
Da suke bayyana takaicinsu kan yaƙin Sudan, ƙasashen biyu sun koka kan halin rashin jinƙai da take ciki, wanda suka ce zai ƙara ta'azzara yanayin rashin jinƙai a yankin, kana suka yi maraba da yunƙurin tabbatar da zaman lafiya a ƙasar cikin diflomasiyya.