Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya yi kira da a hukunta wadanda suke aikata kisan kiyashi a Gaza, yana mai jaddada cewa ba za a ƙyale su su ci bulus ba.
A yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa da aka gudanar a ranar Juma'a a birnin Istanbul tare da mataimakin firaministan kasar Montenegro kuma ministan harkokin wajen kasar Ervin Ibrahimovic, Fidan ya jaddada muhimmancin matsin lamba na kasa da kasa kan Isra'ila ta ba da damar kai agajin jinƙai a Zirin Gaza da kuma hana ci gaba da wahalar da al'ummar Falasdinu.
Fidan ya jaddada goyon bayan Turkiyya ga shari'ar kisan ƙare dangi da Afirka ta Kudu ta shigar da Isra'ila a kotun ƙasa da ƙasa, yana mai jaddada shigar Turkiyya cikin shari'ar. A ranar Larabar nan ne Ankara ta shiga cikin lamarin.
"Yankin ba zai iya jurewa karin tashe-tashen hankula da rikice-rikice, ko yaƙe-yaƙe ba, dole ne a dakatar da Isra'ila," in ji Fidan, yayin da yake aika sakonsa ga ƙasashen da ke goyon bayan Isra'ila ido a rufe tare da samar mata da makamai.
"A bayyane yake an san wanda ke rura wutar ta da hankalin. A daina ɗora wa bangarorin da ba ruwansu. Samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Gabas ta Tsakiya na bukatar jajircewa kan ayyukan Isra'ila. Wadanda ke goyon bayan Isra'ila ido a rufe kuwa suna da hannu wajen kisan gillar da ake yi a Gaza."
Fidan ya jaddada aniyar Turkiyya ta samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin, inda ya jaddada bukatar gaggauta dakatar da manufofin Isra'ila don kauce wa shiga cikin tashe-tashen hankulan da ke faruwa.
Ibrahimovic ya ziyarci Turkiyya ne domin tattaunawa da jami'an Turkiyya kan alakar kasashen biyu da batun Gaza da sauran batutuwa.