Wani jirgi mai saukar ungulu na ɗaukar marasa lafiya ya yi hatsari a lardin Mugla da ke kudu maso yammacin Turkiyya, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum huɗu, kamar yadda gwamnan lardin Idris Akbiyik ya tabbatar.
Matuƙan jirgi mutum biyu da likita ɗaya da wani ma’aikacin lafiya sun rasu a lokacin da jirgin ya faɗa a harabar wani asibiti wanda ke a gundumar Mugla Mentese.
Jami’an kashe gobara da ‘yan sanda da kuma jami’an bayar da agajin gaggawa na Turkiyya sun yi gaggawar isa wurin da lamarin ya faru.
Duk da cewa akwai hazo mai yawa a yankin, amma Akbiyik ya ce har yanzu ba a san dalilin da ya jawo hatsarin ba inda ake ci gana da gudanar da bincike.
Da yake jajanta wa iyalan wadanda suka rasu, Akbiyik ya ce babu wata barna a cikin asibitin.