Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan zai gana da Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres nan ba da jimawa ba domin tattaunawa kan yiwuwar farfado da yarjejeniyar hatsin da aka cimma ta Tekun Bahar Aswad, yana mai bayyana yunkurin a matsayin "muhimmin batu ga daukacin duniya".
"Muna godiya ga wadanda suka ba da gudunmawarsu, Majalisar Dinkin Duniya ta samar da wata sabuwar hanya da za ta taimaka wajen share fagen farfado da shirin Tekun Bahar Aswad, Erdogan ya shaida wa manema labarai a yammacin ranar Litinin a hanyarsa ta dawowa daga birnin Sochi na Rasha.
Yarjejeniyar hatsi ta kasance kan gaba a ganawar da Erdogan ya yi da takwaransa na Rasha Vladimir Putin, wanda a farkon shekarar nan ya janye daga shirin da ya bai wa Ukraine damar fitar da hatsinta daga tashar jiragen ruwa na Tekun Bahar Aswad da ke karkashin ikon Moscow.
Turkiyya da Majalisar Dinkin Duniya ne manyan dillalai a cikin yarjejeniyar hatsi, da aka sanya wa hannu a watan Yulin 2022 a Istanbul.
Erdogan ya kasance a sahun gaba a kokarin farfado da yarjejeniyar wacce ke da matukar muhimmanci wajen tabbatar da samar da abinci a duniya.
Ukraine da Rasha sun kasance manyan kasashen da ke samar da alkama da irin abinci na hatsi a duniya.
Erdogan ya kuma yaba wa kokarin Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya kan batun, yana mai cewa taron shugabannin kasashe da gwamnatoci na duniya da ke tafe a hedikwatar MDD a New York a ranakun 18 zuwa 19 ga watan Satumba zai ba da dama mai kyau don kara tattauna batun.
"Za mu gana da Guterres kuma za mu tattauna wadannan batutuwa a can," a cewar Erdogan.
Bukatun Rasha
Moscow ta ce a shirye take ta tattauna batun cinikin hatsi idan an biya mata bukatunta.
Rasha ta nemi sake hade bankinta na noma cikin tsarin biyan kudaden duniya na SWIFT da kuma samar da inshora ga jiragen ruwa da ke aikin jigilar hatsi zuwa tasoshin jiragen ruwa na Turai.
"Wadannan suna daga cikin sharuddan ci gaba da sayar da hatsi," in ji Shugaba Erdogan.
"Matakan da Majalisar Dinkin Duniya, tare da goyon bayan Turkiyya ne suka kai ga Samar da hanyoyin da za a magance matsalar, ciki har da tsarin sasantawa wanda Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Guterres ya gabatar a ranar 28 ga watan Agusta."
Erdogan ya yi tsokaci game da kalaman Putin kan kiyayyar da kasashen Yamma ke nuna wa Rasha, yana mai cewa, "Idan Turai ba ta cika alkawuran da ta yi ba, Rasha ba za ta dauki wani mataki kan batun cinikin hatsi ba," yana mai nuni da cewa kashi 44 cikin 100 na hatsi na zuwa Turai.
Idan aka kwatanta, kashi 14 ne kawai ke zuwa Afirka. "Kamar yadda kuka sani, hadin gwiwarmu da Rasha yana daga shirin Bahar Aswad, wanda ya ba da gudunmowa sosai ga matsalar abinci a duniya," in ji Erdogan.
Ziyara zuwa Sochi
Erdogan ya ce baya ga yarjejeniyar hatsi, ziyarar tasa ta zuwa Sochi ta ta'allaka ne kan tattaunawa kokarin da Turkiyya ke yi na shiga tsakani a rikicin Rasha da Ukraine, da kuma magance matsalolin abinci a duniya, da kuma hadin gwiwa ta fannin makamashi.
"A shirye muke mu ba da tamu gudunmowar idan kowanne bangare ya amince," in ji Erdogan.
A ganawar da suka yi ranar Litinin, shugaban Turkiyya da takwaransa na Rasha Vladimir Putin sun yi tattaunawa ta mussaman kan alakar da ke tsakanin kasashen biyu, da ci gaban yankin da kuma duniya baki daya.
“Kamar yadda kuka sani, hadin gwiwarmu da kasar Rasha abin misali ne ga shirin Tekun Bahar Aswad, wanda ya taimaka matuka wajen matsalar karancin abinci a duniya,” in ji Erdogan a yayin zantawarsa da manema labarai.
Shugaban ya bayyana matsayin Turkiyya ta fuskar fafutuka don tabbatar da zaman lafiya da kuma samar da tattaunawa ta diflomasiyya dangane da yakin da ake yi a Ukraine.
“Maimakon mu kara ta’azzara matsalar da kuma kara mata wuta, muna kokarin hada bangarorin biyu a wuri guda don cimma manufa guda,” in ji shi.
Erdogan ya ce "babu wanda ya yi nasara a yaki, kuma babu wanda ya yi rashin nasara a cikin zaman lafiya," in ji Erdogan, "A shirye muke mu yi namu aikin a lokacin da bangarorin suka yarda.
Erdogan ya bayyana fatansa na kawo karshen yakin da zaman lafiya mai dorewa bisa dokokin kasa da kasa.
Diflomasiyyar makamashi
A ganawar da suka yi a ranar Litinin, shugabannin kasashen Turkiyya da Rasha sun kuma tattauna kan hadin gwiwa a fannin makamashi.
"Za mu aiwatar da ayyuka daban-daban don isar da kayayyakin makamashi zuwa Turai da duniya ta hanyar kasarmu, sannan kafa cibiyar iskar gas a Turkiyya za ta samar da ci gaba a fannin sufurin makamashi da kuma farashin kayayyaki," in ji Erdogan.
"Kamar yadda muka fada a baya, za mu mayar da kasarmu ta zama cibiyar makamashi da samar da ababen more rayuwa."
Erdogan ya bayyana cewa, nasarorin da kasar ta samu a fannin diflomasiyya ta makamashi sun tabbatar da cewa babu wani abu da za a iya yi a Gabashin Bahar Rum ba tare da Turkiyya ba.