Erdogan ya ce Turkiyya ta gudanar da “fada mafi girma da tasiri” a tarihinta na yaki da kungiyoyin ‘yan ta’adda. Hoto/AA

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya jinjina wa jami’an tsaron kasar bisa ayyukan da suka yi a arewacin Syria da Iraki na dakile kungiyoyin ‘yan ta’adda.

Shugaban ya bayyana cewa dakarun kasarsa “na jiran lokacin da ya dace” domin gudanar wasu ayyukan.

A wata hira da aka yi da shi ta talabijin a ranar Juma’a, Erdogan ya ce Turkiyya ta gudanar da “fada mafi girma da tasiri” a tarihinta na yaki da kungiyoyin ‘yan ta’adda wadanda suke barazana ga tsaron kasar a shekaru 20 da suka gabata.

Erdogan ya bayyana cewa ayyukan jami’an tsaron a ketaren iyakar Turkiyya ya dakile kungiyoyin ‘yan ta’adda wurin samun damar gudanar da ta’addanci a yankuna uku zuwa hudu da ke kan iyakarta, inda ya ce sauran wuraren za a tabbatar da tsaro sannu a hankali.

“Saboda haka, ayyukanmu na kasashen ketare ba su kare ba. Muna jiran lokacin da ya dace ne,” in ji shi.

Turkiyya ta jima tana fama da hare-haren ta’addanci musamman daga kungiyoyin PKK da YPG.

A hare-haren ta’addancin da PKK ta shafe sama da shekara 35 tana kai wa a Turkiyya, kasashen Turkiyya da Amurka da Tarayyar Turai duk sun ayyanata a matsayin kungiyar ta’addanci.

Haka kuma kungiyar ta yi sanadin mutuwar sama da mutum 40,000 ciki har da mata da kananan yara.

Jami’an tsaro na cikin shiri

Turkiyya na daga cikin kasashen duniya na farko da suka ayyana Daesh ko kuma kungiyar IS a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda.

‘Yan ta’addan sun sha kai wa kasar hare-hare. Kungiyar ta kai hare-haren kunar bakin wake akalla 10 sai harin bam bakwai da kuma hari da makami sau hudu, lamarin da ya yi sanadin mutuwar akalla mutum 315 da kuma raunata sama da 100.

Domin mayar da martani, Turkiyya ta kaddamar da shirin yaki da ta’addanci a gida da kuma waje domin kiyaye wasu karin hare-hare.

Da yake magana game da yiwuwar kai hare-hare a lokacin zaben 14 ga watan Mayu na Turkiyya, Erdogan ya tabbatar da cewa “jami’an tsaronmu a halin yanzu suna aiki ba hutawa domin dakile duk wani (yunkurin) harin ta’addanci ko kuma wani lamari da zai tayar da hankali kafin da kuma bayan zabe.”

Masu zabe za su zabi tsakanin Erdogan ko kuma jagoran ‘yan adawa Kemal Kilicdaroglu ko Muharrem Ince ko kuma Sinan Ogan.

Bugu da kari jam’iyyu 24 ne da ‘yan takara masu zaman kansu 151 ne ke neman kujera a majalisar kasar mai wakilai 600.

TRT World