Turkiyya za ta ci gaba da bin diddigin 'yan ta'addar da suka kitsa mummunan hari a Masana'antar Kayan Jiragen Saman Turkiyya da ke Ankara, in ji shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan.
"Babu saurarawa a kudirinmu na yaki da ta'addanci," ya fada wa 'yan jaridu a ranar Juma'a a kan hanyarsa ta dawo wa daga Rasha, inda ya halarci taron BRICS, yana mai jaddada cewar Turkiyya za ta kalubalanci tushen barazanar ta yadda za ta kubutar da makomarta daga ta'addanci.
'Yan ta'addar PKK biyu ne suka kai harin na ranar Laraba, da ya yi ajalin mutane biyar da jikkata wasu da dama, kuma dukkann su an kashe su.
Erdogan ya jaddada aniyar gwmanatinsa na tunkarar ta'addanci tun daga tushe, yana mai kiran hakan da cin fuska kan tsaron kasa na Turkiyya.
"Wannan hari ne kan makomar Turkiyya," in ji shi, yana mai bayyana muhimmancin da masana'antar ta TAI ke da shi.
Da take mayar da martani ga harin, Turkiyya ta kaddamar da farmakan ramuwar gayya. Bayanan sirri sun yi nuni da cewa PKK na da hannu a harin, inda wadanda suka kai harin suka shigo daga Siriya.
Erdogan ya yaba mayar da martani cikin sauri da jami'an tsaron Turkiyya suka yi, yana mai nuni ga an kai farmakai a wurare 40 da ke da alaka da wadanda suka kai harin.
Erdogan ya tafi Kazan na Rasha, sakamakon gayyatar da Shugaban Rasha Vladimir Putin ya yi masa na halartar taron BRICS.
Fadada matakan yaki da ta'addanci
Shugaban na Turkiyya ya yi dogon jawabi na dabaru daban-daban da za su bi don yaki da ta'addanci, wanda ya hado tun daga ayyukan soji da harkokin kudade, da na diflomasiyya.
Manufarmu ita ce Turkiyya da babu ta'addanci a cikin ta" in ji Erdogan, yana nuni ga kokarin da ake ci gaba da yi na kassara kungiyoyin ta'adda a Syria, musamman reshen PKK na Siriya, PYD/YPG.
Ya kuma ce Turkiyya ba da daidaikun mutane kawai take yaki ba, har da manyan kungiyoyi da masu daukar nauyinsu.
Ya ce, "Wadannan kungiyoyin 'yan amshin shata ne kawai," in ji shi, yana mai jaddada cewa, Turkiyya ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen fafutukar tabbatar da 'yancin kai da hadin kan kasa.
Ya kuma bayyana shakkunsa game da amincin Amurka a matsayin abokiyar kawance a wannan fafutuka, yana mai nuni da irin goyon bayan da Amurka ke bai wa kungiyar ta'adda ta YPG a Siriya.
Ƙarfafa ƙungiyar BRICS
Erdogan ya bayyana muradin Turkiyya na zurfafa dangantaka da kasashen BRICS, wanda ke wakiltar kashi 30 cikin 100 na fadin duniya da kuma kashi 45 cikin 100 na al'ummarta, huldar BRICS ta Turkiyya ta yi daidai da kokarinta na kulla kawancen kasa da kasa.
"Sha'awar Turkiyya ga BRICS ita ce haɗin gwiwar tattalin arziki, ba a matsayin madadin NATO ba," in ji shi, yana mai jaddada cewa Turkiyya ta kasance wata gada tsakanin Gabas da Yamma.
A cikin tattaunawar da ya yi da shugabanni, ciki har da Putin da Nicolas Maduro na Venezuela, Erdogan ya binciko yankunan da ke da sha'awar tattalin arziki, yana mai jaddada manufofin Turkiyya na "nasara" a diflomasiyya. "Muna neman haɗin gwiwa bisa mutunta juna da kuma moriyar juna."
Samun ikon cin gashin kai kudi
Wani babban batu a taron na BRICS shi ne samar da "tsarin kudi na madadin dala" ga tsarin duniya na yanzu wanda dalar Amurka ta mamaye.
Erdogan, wanda ya dade yana ba da shawarar rage dogaro ga hanyoyin hada-hadar kudi na Yammacin Duniya, ya sake tabbatar da kudurin Turkiyya na yin ciniki a cikin kudaden kasa a duk inda zai yiwu.
A martanin da ya mayar kan kalaman tsohon shugaban Amurka Donald Trump na baya-bayan nan, wanda ya ba da shawarar ladabtar da kasashen da suke son daina amfani da dalar, Erdogan ya jaddada muhimmancin samun ikon cin gashin kai kudi.
"Manufarmu ba don yin gasa ba ce, sai don mu raba ƙafa," in ji shi. "Kudaden gida a cikin kasuwanci na iya kare tattalin arziki daga firgita daga waje da kuma inganta dangantakar da ta dace."
Matsayar Yammacin Duniya kan batun Gaza
Tattaunawar da Shugaba Erdogan ya yi da shugabannin kasashen duniya a taron na BRICS, ya kuma ta’allaka ne kan karuwar tashe-tashen hankula da Isra’ila ke yi a Gaza da kuma kudancin Lebanon.
"Ba za mu yi shiru ba yayin da ake asarar rayukan marasa laifi," in ji shi.
Erdogan ya yi kakkausar suka ga Ƙasashen Yammacin Duniya, musamman Amurka da Jamus, kan yadda suke ba da tallafin soji ga Isra'ila a cikin abin da ya bayyana a matsayin rikicin bil'adama.
“Kasashen Yammacin Duniya da dama sun yi shiru kan zaluncin da Isra’ila ke yi a Gaza, suna rufe ido saboda laifin da suka aikata a tarihi. Wannan shirun tamkar yana nuna da hadin bakinsu ake komai,” in ji shi. "Ta hanyar kare Isra'ila ko ta halin kaka, suna jefa mutuncin kansu cikin kasada."
Ya kuma yaba wa kasashe irin su Spain, Ireland, da Norway bisa jajircewar da suka bayar ta goyon bayan Falasdinawa. Erdogan ya bukaci mambobin BRICS da su kara goyon bayansu ga ‘yancin Falasdinawa da kuma adawa da ayyukan sojin Isra’ila.
Turkiyya ta yi kamfen na ganin an sanya wa Isra'ila takunkumin sayen makamai da Majalisar Dinkin Duniya ke mara wa baya, saboda tashe-tashen hankula a Gaza da kuma kudancin Lebanon.
Erdogan ya tabbatar da ci gaba da tattaunawa da shugabannin kasashen Turai da suka hada da Giorgia Meloni ta Italiya da jami'ai daga Spain da Ireland, don kafa kawancen da zai takaita wa Isra'ila damar mallakar makamai.
"Dole ne mu takaita samun makamai da ke ba da damar kashe wadanda ba su ji ba ba su gani ba," in ji shi, yana mai fayyace abin da ya kira "Alliance of Humanity" don matsa wa Isra'ila lamba don kawo karshen hare-haren soji.
Sasantawa da Syria
Erdogan ya yi ishara da yiwuwar yin sulhu da gwamnatin Assad na Syria, wanda ke nuna yiwuwar sauyi a manufofin yankin Turkiyya.
Ya yi nuni da cewa, aniyar Turkiyya ta daidaita da Damascus, zai dogara ne kan yadda kasar Siriyan ta yi kokarin kare martabar yankinta da kuma kawar da kungiyoyin ta'addanci a yankin.
"Muna fatan ganin ingantattun matakai na tabbatar da zaman lafiya da kuma cewa Assad ya fahimci fa'idar daidaitawa da Turkiyya," in ji shi, ya kara da cewa ya tattauna da Putin kan matakin hadin gwiwa na Siriya.
Alaƙa da China
Da ya juya kan kasar China, Erdogan ya bayyana dadaddiyar alakar da ke tsakanin kasashen biyu, inda ya mai da su a matsayin magada ga tsoffin al'adun gargajiya da ke da moriyar manyan tsare-tsare.
Yana ganin yuwuwar zurfafa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare da Turkawa da kasar Sin, musamman a fannin ciniki da zuba jari.
Ya ce, "Muna tattaunawa da abokanmu na kasar China kan batutuwa da dama, tun daga kara habaka cinikayya tsakanin kasashen biyu, da karfin zuba jari," in ji shi, yana mai nuni da ziyarar da shugaban kasar Sin Xi Jinping zai kai.