Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bayar da kambunan girmama wa ga ma’aikatan ceto na cikin gida da na waje da suka bayar da gudunmowa wajen kubutar wa da ceton mutanen da girgizar kasa ta rutsa da su a ranar 6 ga Fabrairu, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutum sama da 50,000.
A yayin bukin bayar da kambin shugaban kasa ga mutanen da suka bayar da gudunmowa, Shugaba Erdogan ya ce “A yau, za mu bayar da lambobin girma ga masu aikin ceto da kubutar da mutane na cikin gida da waje saboda sadaukarwar da suka nuna bayan afkuwar girgizar kasa a ranar 6 ga Fabrairu.”
Ya ce, za a bai wa mutum 55,000 lambobin girman saboda sun zama ‘alamar gwagwarmaya’ bayan afkuwar girgizar kasar.
Erdogan ya jaddada cewa tagwayen girgizar kasar na daga cikin munanan ibtila’o’i da dan adam ya fuskanta ba wai a Turkiyya ba har ma a duniya baki daya.
Ya ce “Addu’armu ita ce kar irin wannan mummunan ibtila’i ya sake faruwa a Turkiyya ko a sauran kasashen duniya. Ba ma son kowa ya fuskanci irin wannan abu da muka fuskanta.”
Erdogan ya bayyana cewar “Ma’aikatan ceto 11,320 daga kasashen duniya 90 sun zo Turkiyya bayan afkuwar girgizar kasar, kuma kasashen duniya 60 da kungiyoyin kasa da kasa sun aika da tantuna kusan 250,000 zuwa yankunan, mun san abokanmu na gaskiya.”
Shugaban ya kuma kara da cewa “Za mu ci gaba da kokari har sai dukkan raunukan da girgizar ta janyo sun warke, sannan an kuma rufe duk wani tabo da ta janyo.”