Ina son aika saƙon ta'aziyyata ga masoyansa, waɗanda da yawansu an musu kisan kiyashi," in ji Fahrettin Altun. / Photo: AA

Daraktan hukumar sadarwa ta Turkiyya ya yi tir da "harin gayya da Isra'ila ke kai wa ƴan jarida da kuma ƙoƙarinta na hana watsawa duniya ainihin abubuwan da ke faruwa ga duniya."

"Mun kaɗu matuƙa da sake kashe wani abokin aiki, ɗan jarida Balasɗine Mohammad Abu Hattab da aka yi, tare da iyalansa 11 sakamakon wani harin sama na Isra'ila.

Ina son aika saƙon ta'aziyyata ga masoyansa, waɗanda da yawansu an musu kisan kiyashi a wannan mummunan harin," kamar yadda Fahrettin Altun ya wallafa a shafinsa na X ranar Juma'a.

"Dole a kawo ƙarshen wannan firgicin. Dole 'ƙasashen da suke ganin sun waye' su dawo cikin hankalinsu ta hanyar dakatar da wannan haukar," daraktan sadarwar ya ƙara da cewa.

Da yake tuna wa duniya cewa ya zuwa yanzu an kashe ƴan jarida 38 a munanan hare-haren Isra'ila a Gaza tun 7 ga watan Oktoba, Altun ya ce ci gaba da kashe mutane da ake yi a Zirin Gaza take dokokin hakkin ɗan'adam ne da "ba za a yarda da shi ba."

Da yake magana a kan yadda aka fi kashe yara da mata da tsofaffi da ma'aiktana lafiya da ƴan jarida, Altun ya ce hare-haren Israi'la na kan mai uwa da wabi a kan fararen hula a Gaza ya jawo wani irin mummunan yanayi na kashe dubban fararen hula ba ji ba gani.

"Cin zarafin ɗan'adam da ake yi a Gaza ya kai wani mataki da ba za a iya bayanin muninsa ba, Isra'ila tana kuma ƙoƙarin daƙile duk wata sahihiyar murya da za ta fitar da gaskiyar labarin abin da ke faruwa, ta hanyar kai wa ƴan jarida hari, waɗanda aikinsu kawai suke yi."

Ƴan jarida na cikin babbar barazana

Altun ya yi tuni a kan ƴancin fadin albarkacin baki da na ƴan jarida da kuma ƴancin da al'ummar duniya suke da shi na samun sahihan labarai, inda ya ce Isra'ila "ƙarara ta nuna cewa ɓangarenta kawai take so kafafen watsa labarai su dinga watsawa".

"Ƙasashen duniya sun gaza wajen yin kira ga Isra'ila a kan hare-haren da take kai wa ƴan jarida, amma dole ne ta dakatar da hakan duk da dai ta kashe wasu daga cikin abokan aikinmu," ya ƙara da cewa.

Rundunar sojin Isra'ila ta faɗaɗa kai hare-harenta ta sama da ta ƙasa a Gaza, tun ranar 7 ga watan Oktoba bayan da ƙungiyar Hamas ta kai mata wani harin ba-zata.

Kusan mutum 10,600 aka kashe a rikicin, ciki har da Falasɗinawa 9,061 da kuma Isra'ilawa fiye da 1,538.

Baya ga mace-mace da raba mutane da muhallansu, Isra'ila ta kuma katse ruwa da lantarki da kai fetur Gaza.

Ƴan jarida a Gaza suna cikin barazana sosai a ƙoƙrinsu na bayar da rahotanni a kan munanan hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza, lamarin da ya jawo katsewar sadarwa da lantarki, a cewar Ƙungiyar Kare Ƴan Jarida.

TRT World