Za a kammala jefa kuri'a da misalin karfe biyar na yammaci. Hoto/AA

An soma kada kuri'a a zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokoki a fadin Turkiyya da safiyar Lahadi.

Shugaba Recep Tayyip Erdogan yana neman wani wa’adi sannan daga bangaren adawa, Kemal Kilicdaroglu na Nation’s Alliance da kuma Sinan Ogan na Ata Alliance su ma suna takarar.

Hukumar zaben Turkiyya mai zaman kanta YSK ta sanar da cewa sama da ‘yan kasar miliyan 64 ne suka cancanta su jefa kuri’a a zaben 14 ga watan Mayu, daga cikin har da masu zabe sama da miliyan uku da ke a kasar waje.

Za a kammala jefa kuri’a da misalin karfe 5:00 na yamma a agogon Turkiyya, haka kuma ana sa ran sakamakon farko zai soma shigowa ba da jimawa ba.

Masu zabe a Turkiyya za su nuna katin shaidarsu na dan kasa da sauran katuna da ake bukata a rumfar zabe domin jefa kuri’a.

Daga nan ne ake ba mai zabe takardun jefa kuri’a biyu, daya ta shugaban kasa sai kuma daya ta ‘yan majalisa. Hukumar zaben kasar ta bayyana cewa ba a yarda masu zaben su dauki hoto ko bidiyo ba a wuraren zaben, kuma ana bukatar su bar wayoyinsu a waje.

Bayan an kammala zaben, kuri’un da aka jefa na shugaban kasa ana kirga su a gaban kwamitin zaben wanda ya kunshi jami’an hukumar zaben da kuma wakilan jam’iyyu da kuma jama’ar da suka yi zaben.

Duka ‘yan kasa za su iya zabe

Hukumar zaben Turkiyya ta dauki matakai domin tabbatar da cewa ta sa zaben ya zo da sauki ga duka jama’ar kasar ko da suna da bukata ta musamman.

Ga wadanda ba za su iya barin gidajensu ko kuma gadon asibitinsu ba, akwai akwatunan zabe na tafi-da-gidanka da aka tanadar.

Za a kai wadannan akwatuna inda suke domin ganin cewa sun yi zabensu. Wata mafita kuma ita ce za a iya amfani da motar kwana-kwana ta asibiti domin kai marar lafiya jefa kuri’a a kyauta.

Haka kuma hukumar zaben ta tanadi takardun zabe na musamman ga masu larurar gani. Wadannan takardun suna da gwaragwaran rubutu da kuma haruffan makafi domin su iya zabe ba tare da an tallafa musu ba.

Duka wadannan tsare-tsaren an yi su ne domin tabbatar da cewa duka jama’ar kasar za su iya zabe cikin martaba. An kawo kuri’un ‘yan Turkiyya mazauna kasar waje ta jirgin sama kuma za a kirga su a lokacin daya da wadanda aka jefa a Turkiyya.

An soma jefa kuri’u a kasashen waje tsakanin 27 ga watan Afrilu aka kammala 9 ga watan Mayu.

A babban zaben, dole ne jam’iyya ta samu akalla kashi 10 na kuri’un da aka jefa a fadin kasar kafin dan takararta ya samu kujera a majalisa.

Jam’iyyun hadaka ne kawai za su wuce kashi goma ga jam’iyyunsu su samu kujera. A ranar zabe, an haramta wa duk wata kafar watsa labarai saka duk wata talla ta siyasa ko hasashe ko kuma sharhi kan siyasa har zuwa karfe 6:00 na yamma (1500GMT).

Tsakanin 06:00PM (1500GMT) da 9:00PM (1800GMT), kafafen watsa labarai za su iya wallafa sanarwa kan zabe wadda hukumar zabe ta bayar.

Haka kuma za a haramta sayar da barasa daga 6:00 na safe (0300GMT) zuwa 12:00 na dare (2100GMT), haka an haramta shan giya a bainar jama’a.

TRT World