Turkiyya ta gargadi kasashen Yammacin Turai game da bai wa kungiyar ‘yan ta'adda ta YPG makamai a kasar Syria da sunan yaki da Daesh.
Abubuwa sun sauya a Syria. Muna da yaƙinin cewa nan da lokacin kaɗan za a kawar da ‘yan ta’addan PKK/YOG,” kamar yadda Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya shaida wa taron manema labarai a Ankara.
YPG reshen kungiyar 'yan ta'adda ne PKK ne a Syria, wanda ya shafe shekaru da dama yana tada kayar baya inda ya kashe dubban mutane da suka hada da mata da kananan yara.
Amurka na ci gaba da bai wa YPG goyon bayan soji da kuma kudi, tana mai cewa manufarta ita ce hana sake bullar Daesh.
“Idan kuna (ƙasashen Yamma) da manufofi daban-daban a yankin, idan kuna son samar da wani tsari ta hanyar amfani da Daesh domin ƙarfafa PKK, lallai babu wata hanyar yin haka,” kamar yadda Fidan ya bayyana a wata sanarwar haɗin gwiwa da takwaransa na Jordan Ayman Safadi.
Fidan ya kuma bayyana cewa ana dab da kawo ƙarshen gallazawar da PKK ke yi wa Kurdawa.