A watannin Janairu da Fabrairun 2023, an samu karin fasinjoji miliyan 4.82 da aka yi jigilar su a filayen tashi da saukar jiragen sama na Istanbul, sama da na watannin a shekarar 2022, inda adadin ya kama miliyan 15.97.
Bayanan da aka fitar a shafin yanar gizon Hukumar Kula da Filayen Tashi da Saukar Jiragen Sama na Kasa sun bayyana cewa kimanin fasinjoji miliyan 10.76 sun yi amfani da filin tashi da saukar jiragen sama na Istanbul a watanni biyu na farkon wannan shekarar.
Miliyan 8.37 na fasinjojin na kasa da kasa ne, yayin da miliyan 2.39 kuma na cikin gida.
Adadin matafiya a filin tashi da saukar jiragen saman Istanbul ya karu da fasinjoji miliyan 3.72 idan aka kwatanta da na watanni biyun farkon shekarar da ta gabata, wanda aka samu fasinjoji miliyan 7.44, da suka hada da na kasa da kasa miliyan 5.18 da na cikin gida miliyan 1.85.
A watannin Janairu da Fabrairun bana fasinjoji miliyan 5.20 ne aka yi jigilar su a filin tashi da saukar jiragen saman Sabiha Gokcen.
Daga cikin su an samu fasinjoji miliyan 2.47 na cikin gida da miliyan 2.72 na kasa da kasa.
Adadin fasinjojin kasa da kasa da aka yi jigila a Sabiha Gokcen ya karu da kashi 36 yayin da na cikin gida ya karu da kashi 18 cikin 100 idan aka kwatanta da na watanni biyun farkon bara.