Dakarun Turkiyya na ci gaba da yakin da 'yan ta'adda ba kakkautawa, in ji Zeki Akturk, kakakin Ma'aikatar Tsaron Kasa ta Turkiyya a yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a ma'aikatar.
Akturk ya yi karin haske kan farmakan da ake ci gaba da kai wa kungiyoyin ta'adda daban-daban da suka hada da PKK/KCK/PYD-YPG, Daesh, da FETO, a cikin kasa da kan iyakokinta.
Ya bayyana cewa a mako dayan da ya gabata kawai, an kassara 'yan ta'adda 63 a farmakan da aka kai, wanda ya kawo adadin wadanda aka kassara daga 1 ga janairu zuw ayanzu ya kama 2,541.
Da yake jaddada nasarar da ake samu wajen hana tsallaka iyaka ba bisa ka'ida ba, ya bayyana cewa a mako dayan da ya gabata an kama 'yan ta'adda 188 da suka hada da mambobin FETO 6 da na Daesh 1, inda aka kuma dakatar da wasu 3,441 daga tsallaka iyakar.
Ya ce tun daga farkon 2024, an kama mutane 686, an kuma dakatar da 18,594 daga tsallaka iyaka ba bisa ka'ida ba.
Ya kuma jaddada yunkurin da ake yi na tabbatar da tsaro da inganci iyakokinsu da kuma kokarin da ake ci gaba da yi na magance barazanar 'yan ta'adda a ciki da wajen Turkiyya.
Tun shekarar 2016 Turkiyya ta kaddamar da farmakai uku da aka samu nasarar kakkabe 'yan ta'adda daga iyakokinta da arewacin Siriya, da manufar hana kafa matattarar 'yan ta'adda.
A hare-haren ta'addanci da ta dauki shekara 35 tana kaiwa a Turkiyya, kungiyar PKK da Turkiyya da Amurka da Ingila da Tarayyar Turai suka bayyana a matsayin ta ta'addanci, ta yi ajalin sama da mutum 40,000 da suka haɗa da mata da yara ƙanana da jarirai.