Altun ya ce yakin da Isra'ila ke yi na ta'addanci da kashe fararen hula a Gaza ya riga ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula fiye da 18,000. Hoto: OTHERS

Daraktan Sadarwa na Turkiyya Fahrettin Altun ya yi kakkausar suka kan hare-haren da Isra'ila ke kai wa 'yan jarida, yana mai zargin Tel Aviv da ƙoƙarin ɓoye ɓarnar da ta janyo a Gaza ta Falasdinu ta hanyar tsoratar da 'yan jarida.

Kalaman na Altun sun zo ne bayan da wani dan jarida mai daukar hoto na kamfanin dillancin labarai na Anadolu Mustafa Alkharouf, wanda ke Gabashin Birnin Ƙudus da aka mamaye domin aiki, ya samu mummunan rauni lokacin da sojojin Isra'ila suka kai masa hari a ranar Juma'a, har a kwantar da shi a asibiti.

A shafinsa na X, Altun ya wallafa saƙon Allah wadai da harin da aka kai kan fararen hula wanda ya yi sanadin mutuwar 'yan jarida sama da 60, tare da yi wa Alkharouf fatan samun sauƙi cikin gaggawa.

Ya kara da cewa, "Sojojin Isra'ila sun ƙi yin wani abin da ya dace don kare 'yan jarida, Maimakon haka, sun fi sha'awar hana ma'aikatan watsa labarai yin ayyukansu domin ba da labarin gaskiya daga tushe."

Da yake zargin Isra’ila da saba ka’idojin kasa da kasa da ke kare ‘yancin jama’a na samun sahihin bayanai, Altun ya ce Isra’ila ta yi “kokarin boye barnar da ake yi a kasa ta hanyar tsoratar da ‘yan jarida” a kokarin rage martanin kasashen duniya."

Ya kara da cewa "Kokarin da suke yi na ganin an kawar da laifukan yaki a Gaza ba zai yi nasara ba. Duniya ta riga ta ga hakan saboda jajircewar ma'aikatan watsa labarai da ƙwararrun ƴan jarida."

An kashe Falasdinawa 18,787

Altun ya ce yakin da Isra'ila ke yi na ta'addanci da raba fararen hula da muhallansu a Gaza ya riga ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula fiye da 18,000.

Isra'ila tana ta ruwan bama-bamai ta sama da ta ƙasa, ta kuma yi wa Gaza ƙawanya, sannan ta kai farmaki ta ƙasa a matsayin ramuwar gayya kan harin ba-zata da Hamas ta kai mata a ranar 7 ga watan Oktoba.

Aƙalla Falasdinawa 18,787 aka kashe tun daga lokacin, sannan 50,897 ne suka jikkata a harin da Isra’ila ke kaiwa, a cewar hukumomin lafiya na Gaza.

Adadin mutanen da Isra'ila ta kashe a harin na Hamas ya kai 1,200, yayin da kungiyar Falasdinawan ta yi garkuwa da wasu 135 a Gaza, a cewar alkaluman hukuma.

TRT World