Türkiye Election/Photo AA

Za a gudanar da zabukan shugaban kasa da na 'yan majalisar dokokin Turkiyya ranar 14 ga watan Mayu, inda Jam'iyyar AK ta Shugaba Recep Tayyip Erdogan ke neman ta-zarce.

Jam'iyyar adawa ta zabi Kemal Kilicdaroglu, shugaban Jam'iyyar CHP, a matsayin dan takarar shugabancin kasarta.

Ga dai abu shida da suka kamata ku sani kan tsarin zaben Turkiyya:

1. Yanayin zaben

Yanayin zaben Turkiye ya rabu gida biyu, inda ake samun shugabanni ta hanyar kaso da kuma ta hanyar rinjayen kuri’u.

Batun samun nasara ta hanyar kaso zai zama jam’iyyu za su iya samun kujeru a majalisa ta hanyar iya kason da suka samu na kuri’u.

Ana kuma amfani da kuri’u mafi rinjaye a zaben shugaban kasa inda ake nufin dole wanda zai zama shugaban kasar ya samu sama da rabin kuri’un da aka jefa a fadin kasar.

2. Zabe iri biyu

Zaben da ake yi a kasar iri biyu ne, na farko shi ne a zabi shugaban kasa na biyu kuma a zabi ‘yan majalisa.

3. Abubawan da ake bukata don shiga zaben:

Domin shiga zaben ‘yan majalisa, dole ne jam’iyya ta samu akalla kashi bakwai cikin 100 na jumullar kuri’un da aka jefa a kasar, kamar yadda sabuwar dokar da aka saka wa hannu a Afrilun bara ta bayyana.

Dokar ta yarda jam’iyyu su yi maja ko su hada kansu. Hakan na nufin kowace jam’iyya idan ta kulla kawance za ta iya samun kujera a majalisa amma sai sun samu sama da kashi bakwai cikin 100 na kuri’u a kowace gunduma da ke Türkiye.

4. Gundumomin da ake zabe:

Akwai gundumomi 87 da ake zabe a Türkiye. Adadin ‘yan majalisar da ke wakiltar kowace gunduma ya sha bamban saboda adadin jama’a.

Misali, Istanbul na da ‘yan majalisa 98 sakamakon shi ne birnin da ya fi kowane yawan jama’a a kasar.

Sai Ankara babban birnin kasar yana da ‘yan majalisa 36, sai kuma lardunan Tunceli da Bayburt duka suna da ‘yan majalisa daya kowace.

5. Jam’iyya kadai ake iya zaba:

Hakan na nufin masu zabe za su iya zaben jam’iyya ne kadai; masu zabe ba su da tasiri kan yadda jam’iyya ta tsara sunayen ‘yan takarar da za a zaba.

6. Zabar shugaban kasa:

‘Yan Turkiye na yin zaben shugaban kasa daban da na ‘yan majalisa, inda ake zabe har zuwa zagaye na biyu.

Idan babu wani dan takara da ya samu kuri’u mafi rinjaye a zagaye na farko, ‘yan takara biyu da suka fi samun yawan kuri’u na zuwa zagaye na biyu inda dole daya daga ciki ya samu sama da kashi 50 cikin 100 na kuri'u domin ya zama zababben shugaban kasa.

TRT World