A zaben shugaban kasa da 'yan majalisar dokoki na ranar 14 ga Mayu 'yan kasar Turkiyya a kasashen duniya 72 sun jefa kuri'a / Photo: AA

Jam’iyyar AK mai mulki a Turkiyya ta yi suka da babbar murya ga Ministar Belgium Zuhal Demir, bayan ta yi kiran da a cire damar zama dan kasashe biyu na 'yan kasar Turkiyya saboda kawai sun zabi Shugaba Recep Tayyip Erdogan a zaben da ya gabata.

“Yar siyasar ta gamu da fushin Jam’yyar AK bayan ta bayar da shawarar a cire ‘yan Turkiyya daga zama ‘yan kasar Belgium saboda mafi yawan su sun zabi shugaban kasar Recep Tayyip Erdogan a zaben da ya gabata.

Ministar Daidaiton Hakki da Yaki da Talauci a gwamnatin yanki a Belgium Zuhal Demir, wadda ita kanta 'yar asalin Turkiyya ce, ta ce “Erdogan ya fi samun karbuwa a Belgium sama da Turkiyya. Ya samu kaso 72 na kuri’un Turkawan kasar.”

Ta kara da cewa “Turkawa da ke Turai na yin wata wauta wajen zabe. Babban abin yi don maganin ‘yan Turkiyya a yankinsu shi ne a hana su damar zama ‘yan kasashe biyu, ko a rage martabar damar zuwa kawai ta je-ka-na-yi-ka yadda ba za ta bayar da damar jefa kuri’a ba.”

Demir mamba ce ta sabuwar jam’iyyar Kawancen Yankin Flemish (N-VA), jam’iyyar ‘yan kishin kasa masu ra’ayin rikau a Belgium.

Kafafen yada labarai na Turkiyya sun bayyana cewa, Zuhal diya ce ga wasu Turkawa da suka yi gudun hijira zuwa Belgium kuma an haife ta a kasar. A baya ma ta taba yin bayanin nuna adawa ga damar zama dan kasashe biyu, ta kuma fita daga zama ‘yar kasar Turkiyya a 2017.

Mai magana da yawun jam’iyyar AK Omer Celik, ya fitar da wani sako ta shafin Twitter yana mayar da martani ga Demir “Wadda ta nufi ‘yan kasarmu da ke kasashen waje. Muna suka da babbar murya ga wannan kalami. Babban kuskure ne a ce Ministar Tarayyar Turai ce ke amfani da yaren nuna wariya na dokar Turai.”

Celik ya kara da cewa “Dukkan ‘yan kasarmu za su sake bayar da amsa ga wannan jirkitaccen tunanin a akwatin zabe.

"‘Yan kasarmu da suka san irin gwagwarmayar da Shugaba Erdogan ke yi, za su mayar da martani da bayar da amsar da ta dace tare da koyar da darasi ga wannan jirkitaccen tunani ta hanyar nuna kakkarfan goyon baya ga Shugaba Erdogan.”

Sauka daga layi

Kakakin shugaban kasar Turkiyya Ibrahim Kalin ma ya mayar da martani kakkausa ga kalaman na Demir, inda ya ce Demir ta yi kuskure, kuma ‘yan kasar Turkiyya da ke Turai za su sauke nauyinsu na zabar shugaban kasar Turkiyya.”

A sakon da ya fitar ta shafin Twitter, Kalin ya rubuta cewa ”Sun dimauta tare da rasa fahimta, inda har suke shawartar kwace ‘yancin ‘yan kasarmu da ke rayuwa a kasashen waje saboda sun zabi shugaban kasarmu.”

Ya ce, wannan na zuwa ne daga bakin ministar kasar da ke mamba a Tarayyar Turai.

“Za ki zama alkaliya.”

“Yan kasarmu da ke rayuwa a kasashen waje za su bayar da amsa mafi dacewa ga wannan kalaman”.

TRT World