Shugaba Erdogan ya kara da cewa Turkiyya za ta samar da manyan sabbin birane biyu daban-daban a Istanbul wanda kowanne zai dauki mutum miliyan daya /Hoto: AA

Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yaba nasarorin da gwamnatinsa ta samu game da ayyukan sake gina yankuna da dama da ake yi bayan mummunar girgizar kasar da ta afku a ranar 6 ga Fabrairu.

Nasarorin sun hada da ci gaban samar da makamashi da dabbaka manufofin kasashen waje, inda ya kuma lissafo manufofin da suke son cimma a nan gaba, a daidai lokacin da kasar ke shirin babban zaben 14 ga Mayu.

A wata tattaunawa da ya yi da tashar TRT, Shugaba Erdogan ya kuma bayyana damuwarsa game da halin siyasar da ake ciki a Tunisiya da Sudan.

Da yake tabo batun sake gina yankuna a Turkiyya bayan mummunar girgizar kasar da ta afku, Erdogan ya ce sake gina yankunan da ibtila’in ya shafa ne babban abun da suka bai wa fifiko.

Shugaban na Turkiyya ya kuma ce gwamnati tana amfani da dukkan damarmakin da ke hannun ta wajen sake gina yankunan, kuma za a magance wa kowa matsalarsa a yankunan.

Ya ce “Za mu tabbatar da an kare hakkokin wadanda girgizar kasa ta shafa. Ana sake gina gidajen da ma ba su rushe gaba daya ba.”

Game da batun rage cunkoso a Istanbul babban birnin kasuwanci da hada-hadar kudi da raya al’adu mafi girma a kasar, Erdogan ya bayyana cewa “Ba za mu bayar da dama karin jama’a su yi tururuwa zuwa Istanbul ba.

Za mu rarraba jama’a zuwa yankunan birnin da ba sa fuskantar barazanar girgizar kasa.”

Shugaba Erdogan ya kara da cewa Turkiyya za ta samar da manyan sabbin birane biyu daban-daban a Istanbul wanda kowanne zai dauki mutum miliyan daya.

Kuma an fara ayyuka a yankuna bakwai da aka ware a wasu garuruwan don samar da matsugunai.

Da aka tambaye shi game da Cibiyar Kudi ta Istanbul da aka kafa kwanan nan, Erdogan ya ce suna da manufar mayar da cibiyar ta zama daya daga cikin 10 mafi girma a duniya.

TRT World