Ana sa ran yin damben a wannan karon a birnin Riyadh. Hoto/Getty Images

Kasar Saudiyya za ta karbi bakuncin dambe ajin babban nauyi tsakanin Tyson Fury da Oleksandr Usyk.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa an saka hannu kan damben wanda ake sa ran karawa a birnin Riyadh na Saudiyya.

Sai dai ba a bayyana takamaimai ranar da za a gwabza tsakanin gwarazan biyu ba.

Fury dan asalin Birtaniya mai shekara 35 ya kasance gwarzo wanda yake rike da kambun WBC inda Usyk dan kasar Ukraine ke rike da kambunan WBA da WBO da IBF.

Duk wanda ya yi nasara a yayin damben za a nada shi a matsayin gwarzo wanda ya lashe duka kambuna hudu, wato WBC da WBA da WBO da IBF.

Ana hasashen cewa watakila a yi damben a watan Disamba ko kuma a matsar da shi zuwa farkon shekarar 2024.

Fury ya yi nasara a dambe 33 inda ya yi kunnen doki sau daya tun bayan da ya zama kwararren dan dambe a 2008.

Oleksandr Usyk ya yi kokarin cin duka dambensa 21 inda kuma ya kare kambunansa a watan Agusta a damben da ya kara da Daniel Dubois.

Haka kuma a bara Usyk ya kare kambunansa bayan doke Anthony Joshua wanda aka yi a birnin Jeddah na Saudiyya.

Reuters